✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Rikicin PDP: Akwai fahimtar juna tsakanina da su Wike – Gwamnan Bauchi

Hakan dai na alamta barakar da ke tsakanin Gwamnan da Atiku

A wani yanayi da ke nuna tsamin dangantaka tsakaninsa da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce akwai shakuwa mai karfi tsakaninsa da gwamnonin PDP su biyar da ba sa ga-maciji da Atiku.

da ake yiwa lakabi da ‘G5’.

Mohammed ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi sa’ailin da ya karbi bakuncin Gwamnonin da ake yi wa lakabi da ‘G5’, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a masaukin Shugaban Kasa da ke Bauchi babban birnin jihar, ranar Laraba.

Gwamnonin da suka hada da; Nyesom Wike na Ribas da Samuel Ortom na Binuwai da Okezie Ikpeazu na Abiya da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, in ban da Seyi Makinde na Oyo da bai samu halarta ba sakamakon ba ya kasar.

Mohammed ya ce ya ji dadi matuka da ziyarar takwarorin nasa, inda ya ce, “Ya kamata a ce ina cikinsu amma sun hana ni saboda wasu dalilai.

“Amma akwai shakuwa mai karfi a tsakanina da su. Babu ranar da ba na kira in yi magana da kowannensu.

Ya kara da cewa, ita siyasa harka ce mai bukatar ka tafi tare da mutanen da naku ya zo daya.

Ya ce zaben fidda gwanin takarar Shugaban Kasa da suka shiga ya kara kusanta su tare da takwaran nasa.

Tun farko, jagoran tawagar, Gwamna Wiki ya ce, “Mun zo ne don nuna goyon baya ga abokinmu Gwmanan Jihar Bauchi.

“Muna sane zai nemi wa’adin mulki na biyu, kuma abin da mukan yi ga abokanmu shi ne mu bincika mu san halin da suke ciki. Wannan shi ne lokacin da ya dace mu kasance da abokanmu.

A ranar Laraba gwamnonin suka dira Babban Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa inda inda Gwamna Baka kansa ya tarbe su.