Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ce ba ta kasance ’yar amshin shata ga Kasashen Yamma ba dangane da rikicin juyin mulki da ya dabaibaye Jamhuriyyar Nijar.
ECOWAS na wannan batun ne don yi watsi da zarge-zargen cewa wasu ne daga ƙasashen waje ke ingiza ta a kan lallai sai tilasta wa sojojin Nijar, mayar da ƙasar kan tafarkin tsarin mulki.
- Ba don mu ba da wasu kasashen Afirka sun rushe — Faransa
- Za mu dauki fansar dakarun da aka kashe a Neja — Rundunar Soji
“ECOWAS, ƙungiyar ƙasashe ce mai aiki da dokoki da tsare-tsare, ƙa’idoji da ladubban da suka kafa ta.
“Muradinmu shi ne mu kare haƙƙoƙin al’ummarmu,” Omar Touray, shugaban hukumar ECOWAS ya ce a lokacin wani jawabi da ya gabatar a Abuja, babban birnin Najeriya.
Omar Touray ya ƙara da cewa ECOWAS ba ta ƙaddamar da yaƙi a kan al’ummar Nijar ba, yayin da ake fuskantar barazana kan yiwuwar amfani da ƙrfin soji da nufin mayar da shugaban ƙasar wanda aka zaɓa a kan tafarkin dimokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar ba ta da niyyar mayar da Nijar, ƙasar da za a ruguza.
“ECOWAS ba za ta taɓa barin al’ummar Nijar su sha wahala a hannun maƙiya a cikin gida da kuma ƙetare ba.
“Kawai dai ECOWAS ta damu ne da abin da zai kyautata rayuwar al’ummar Nijar.”
Omar Touray ya ce ECOWAS za ta yi amfani da “duk wata dama da take da ita” don mayar da zaman doka a ƙasar.
Ya ƙara da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yuli tun farko “sun bijire wa duk wani ƙoƙarinmu na diflomasiyya” kuma ya ce “ba za a taɓa amincewa da” mulkin riƙon ƙwarya tsawon shekara uku da sojojin juyin mulkin suka sanar ba.