✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin nadin sarauta ya yi ajalin dagaci a Neja

Kafin faruwar wannan lamari, sai da aka kone gidansa a shekarar da ta gabata.

Wasu masu tayar da zaune tsaye sun kashe dagacin kauyen Lambata da ke Karamar Hukumar Gurara a Jihar Neja, Alhaji Mohammed Abdulshakur Lambata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an fara kai wa dagacin hari ne da safiyar ranar Asabar yayin da ya halarci wani taro amma ya tsallake rijiya da baya.

Dansa mai suna Zakari Musa, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa maharan sun kashe mahaifin nasa ne ta hanyar sara da adduna da duka da bulalai, kuma nan take ya ce ga garinku nan.

“Har gida maharan suka biyo shi suka kashe shi.

“Da safiyar ranar Asabar suka fara kai masa harin yayin da halarci wani taro a hedikwatar Karamar Hukumar Lambata, amma ya tsallake rijiya da baya.

“Sai suka [maharan] sake biyo shi har gida da misalin karfe 1 na rana, suka kashe shi da adduna, sanduna da sauran miyagun makamai.

“Kuma duk wannan lamari ya faru ne saboda nadin sarauta da Sarkin Suleja ya yi masa shekaru uku da suka gabata.

“Masu adawa da shi na ganin su ya kamata su gaji sarautar don haka bai cancanci rawanin ba, har dai zuwa yanzu da aka yi ta fadi-tashi suka kashe shi.

‘Tun ba yanzu ba ake son ganin bayansa’

“Kafin faruwar wannan lamari, sai da aka kone gidansa a shekarar da ta gabata,” inji Zakari

Ya kara da cewa, sai da kanin mahaifinsa ya rasa ido daya a sanadiyar harin sannan kuma wani kaninsa ya samu karaya a hannu.

Kazalika, ya ce mutane da dama sun samu raunuka daban-daban wadanda suka yi jinya a Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna, babban birnin jihar.

Zakari ya zargi jiga-jigan Karamar Hukumar Lambata da hannun a kisan mahaifinsa, yana mai cewa “a makon jiya Shugaban Karamar Hukumar ya bayar da umarnin dakatar da biyansa albashi. ”

Aminiya ta ruwaito cewa, an dauki tsawon shekaru uku ana wannan rikici tun bayan da Sarkin Suleja, Mallam Awwal Ibrahim ya nada marigayin a matsayin dagacin kauyen Lambata, lamarin da ya rika haddasa tashin-tashina daga bangarorin da ke ganin gajiyar sarautar ta su ce

Rundunar ’yan sandan Jihar Neja, ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta, DSP Wasiu Abiodun.

An sanya dokar hana fita a kauyen

Haka kuma, Gwamna Abubakar Sani Bello ya sanya dokar hana fita a kauyen a matsayin wani yunkuri na tabbatar da kiyaye da doka da oda.

Cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane ya fitar, ya ce dokar hana fitar za ta fara aiki ne daga karfe 6 na Yamma zuwa 6 na safe daga ranar Lahadi, 15 ga watan Janairun 2023.

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi Allah wadai da kisan dagacin, yana mai umartar jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya a kauyen.