✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na Kashe wa Ummita N120m —Dan China

Kanwar Ummita ta siffanta yadda dan China ya yi wa marigayiyar kisan gilla a kan idonsu, a cikin gidansu

Dambarwar karbar Naira miliyan 120 daga hannun dan kasar China da ake zargi da kashe budurwarsa a Kano ta Kunno kai a yayin da kanwarta ta bayyana wa kotu yadda wanda ake zargin ya yi wa marigayiyar kisan gilla a kan idonsu, a cikin gidansu.

A ci gaba da gurfanar da Mista Geng Quangrong wanda ake zargi da kashe Ummu Kulsum (Ummita) ne aka yi wa kanwarta Asiya, tambaya kan Naira miliyan 117 da wanda ake zargin ya tura wa marigayiyar ta banki a matsayin kudin shirye-shiryen aurensu.

Lauyan Mista Geng Quangrong, Barista Muhammad Danazumi ya kuma tambayi Asiya game ko ta san cewa Mista Geng ya saya wa marigayiyar sarkoki na Naira miliyan 3.3.

Ya kuma tambaye ta ko Mista Geng wanda suka shekara biyu suna soyayya da Ummita yana ba marigayiyar Naira dubu 100 a matsayin kudin kashewa a duk mako.

Sai dai Asiya ta bayyana wa kotun cewa ba ta da masaniya a kan duk wadannan batutuwa.

Yadda dan China ya kashe ’yata —Mahaifiyar Ummita

Tun da farko a zaman kotun na ranar Laraba, mahaifiyar marigayiyar ta shaida wa kotun cewa lokacin da Mista Geng ya zo gidansu ya buga kofar gidan da karfi, hakan ya sa ta je ta bude masa kofa inda ya hankade ta gefe ya shige cikin gidan da sauri ya je ya sami marigayiyar ya caccaka mata wuka, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.

An kan idonmu ya kashe ta —Kanwar Ummita

Haka kuma masu gabatar da kara sun gabatar da kanwar marigayiya, Asiya Sani a matsayin shaida ta biyu inda kuma ta gaya wa kotun cewa tana ta ga lokacin da Mista Geng Quangrong ya caccaka wa yayarta wuka lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta

Asiya ta ci gaba da shaida wa kotun cewa a ranar 16 ga watan Satumba, 2022 misalin karfe 9 na dare, Mista Geng ya zo gidansu yana buga kofar da karfi sai mahaifiyarta ta tafi don sanin wanda ke buga kofar inda marigayiyar ta gaya mata cewa dan China ne ke bug kofar.

Ta bayyana cewa lokacin da mahaifiyarta ta bude kofar sai ta gan shi a kofar, inda ya bangaje ta tare da yin saurin shigewa cikin gidan ya sami Ummmulkulsum, inda ta yi masa gargadin cewa za ta kira masa ’yan sanda.

“Lokacin da ’yar uwata ta shiga cikin daki tana yin waya sai ya bi ta ciki ya kulle kofar cikin daki inda kuma muka leka cikin daki ta taga muka ga ya rike wuka ya yi kan marigayiyar a kan gado ya caka mata wukar,” in ji.

Asiya Sani ta bayyana cewa hakan ya sa cikin tsoro ta bar wurin tagar ta fara ihu inda ita kuma mahaifiyarsu ta fita waje tana neman taimako.

“Daga nan sai Mista Geng ya fito daga cikin dakin ya bar ’yar uwata kwance cikin jini.

“Daga bisani kuma makwabta suka shigo suka kama shi inda suka damka shi hannun ’yan sanda.

“Ni da wasu mutane biyu kuma muka dauki ’yar uwata muka kai ta asibiti sai dai daga fahimtarmu tun kafin mu isa asibiti rai ya yi halinsa.”

%d bloggers like this: