✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Masarautu: Gwamnatin Kano ta ba wa Ribadu hakuri

Gwamnatin Kano ta bukaci Shugaba Tinubu ya sa baki kan dambarwar masarautun jihar mai cike da rudani

Gwamnatin Kano ta ba wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu hakuri kan zargin hannunsa a rikicin masarautun jihar.

Aminiya ta ruwaito mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam a ranar Asabar yana zargi Ribadu da yunkurin dawo da Alhaji Aminu Ado Bayero kan kujerar Sarkin Kano bayan gwamnatin jihar ta sauke shi tare da sauran sarakunan jihar.

Daga bisani Ribadu ya nesanta kansa da kuma ofishinsa daga rikicin, sannan ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu.

Bayan haka ne mataimakin gwamnan ya ba da hakuri ga Ribadu yana mai cewa yaudarar gwamnatin aka yi da bayanan da aka ba ta.

“Mun kara zurfafa bincike inda kuma gano cewa yaudarar mu aka yi, saboda haka, a madadin gwamnatin Kano, mana ba da hakuri ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro,” in ji mataimakin gwamnan.

Gwamnatin jihar ta kuma bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki kada abin ya kara rincabewa fiye da haka.