Gamayyar Malaman Addinin Musulunci a Jihar Kano, sun buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki ƙwararan matakai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Malaman sun nuna yadda jihar ta yi ƙaurin suna wajen zaman lafiya duk da ƙalubalen siyasa da ta fuskanta, Malaman sun bayyana damuwarsu kan abubuwan da ke faruwa game da dambaruwar masarauta a jihar.
- Abin da ya sa na fara aikin DJ a Kano — Kyauta Dillaliya
- Shugabannin tsaro sun gana da Sanusi da Abba a fadar Sarkin Kano
Malaman sun jaddada wajabcin haɗa kai da gwamnatin jihar domin daƙile tashe-tashen hankula biyo bayan gyaran da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautar Kano.
Gyaran dokar da majalisar ta yi wadda gwamnan ya amince da ita, ta haifar da cece-kuce, bayan da kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da sarakunan.
Malaman sun bayyana cewar akwai buƙatar wanda aka take wa haƙƙi ya nemi haƙƙinsa a kotu ba tare da tashin hankali ba.
Sun buƙaci dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa da su mutunta doka tare da kaucewa duk wani abu da zai iya tada tarzoma.
Malaman sun ja hankalin shugaban ƙasa kan aikin da ya rataya a wuyansa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar nan.
“Muna kira ga mai girma shugaban ƙasa da ya bai wa al’ummar Jihar Kano damar magance waɗannan matsaloli cikin ruwan sanyi ba tare da yin amfani da ƙarfi ko asarar rayuka ba,” in ji sanarwar.
“A matsayinmu na manyan masu ruwa da tsaki a jihar, muna so mu tabbatar wa shugaban ƙasa cewa za mu tuntuɓi duka ɓangarorin don samar da zaman lafiya.”
Waɗanda suka rattaba hannu kan sanarwar sun haɗa da Shaihu Abdullahi Uwais Limanci, Shaykh Ibrahim Khalil, da Farfesa Muhammad Babangida Muhammad, sun jaddada ƙudirinsu na tabbatar da zaman lafiya.
Malaman sun kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.