✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma na jawo asarar biliyan N4.8 a Najeriya

An yi kiyasin cewar Najeriya na rasa Naira biliyan 4.8 ($12billion) a duk shekara sakamakon rikicin manoma da makiyaya a yankin Arewa ta tsakiya. Daraktan…

An yi kiyasin cewar Najeriya na rasa Naira biliyan 4.8 ($12billion) a duk shekara sakamakon rikicin manoma da makiyaya a yankin Arewa ta tsakiya.

Daraktan Kungiyar Mercy Corps a Najeriya, Ndubisi Anyanwu, ya bayyana haka bayan tattaunawarsu da jami’an gwamnatin jiha da kananan hukumomin Jihar Binuwai, a garin Makurdi.

Anyanwu ya ce “Mun kimanta asara ta akalla Dala miliyan 12 da ake yi a duk shekara sakamakon rikicin manoma da makiyaya. Wanannan matsalar na iya shafar ko’ina a Najeriya”.

Ya kara da cewar daukar mataki kan rikicin makiyaya da manoma da ke faruwa a yankin na da matukar muhimmanci, wanda hakan ya tilasta kungiyar shiga yankin.

Kungiyar ta Mercy Corps, a cewarsa, za ta gudanar da aikin wata 60 a jihar Binuwai da wasu jihohin Najeriya karkashin tallafin USAID da hadin kan jihar.

Anyanwu ya ce, za su tattauna da gwamnatin jihar a kan matsalolin da ke kawo rikicin tare da aiwatar da abubuwan da za su kawo zaman lafiya cikin gaggawa.

“A yanzu haka, mun yaba da kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya”, inji Darektan.

A bayanan da Shugabannin Kananan Hukumomin suka yi, sun bayyana cewar rikicin manoma da makiyaya da matsalolin matasa da rashin samar da ababan more rayuwa na daga cikin ababen da ke da bukatar a kawo musu dauki.