✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 12 a Taraba

Lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Takum da ke Jihar

Wani rikici da ya ɓarke tsakanin makiyaya da manoma ya yi ajalin manoma 10 da makiyaya 2 a ƙauyen Jenuwa na Ƙaramar Hukumar Takum a Jihar Taraba.

Rahotanni sun nuna an kashe manoman ne waɗanda dukkansu ’yan uwan juna ne lokacin da suke hanyarsu ta zuwa gona domin yin girbi a ranar Juma’a.

Aminiya ta gano cewa an yi wa manoma kwanton-ɓauna ne a kusa da gonar tasu.

Shugaban kungiyar ’yan ƙabilar Kutep na Kasa, Emmanuel Ukwen ya shaida wa Aminiya cewa dukkan manoman da aka kashe ’yan ƙabilarsu ne.

Ya kuma zargin cewa ’yan kwanakin kafin wannan harin, makiyayan sun kuma kai musu hari inda suka kashe matasa biyu, sannan suka yi wa wata mata fyade.

Ya ce bayan haka ne su ma suka kaddamar da harin ramuwar gayya, inda suka kashe makiyaya biyu, suka raunata wasu biyu.

Emmanuel ya kuma yi zargin cewa bayan waccan ramuwar gayyar ce shi ne makiyayan suka kuma dawowa suka kashe musu mutum 10 a ranar Juma’a

Sai dai a cewar shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah, reshen Kudancin Taraba, Ya’u Ibrahim Barewa, matasa sun tare mutanensu hudu da ke kan hanyar Takum zuwa Kashinbila, inda suka kashe biyu daga ciki, suka kuma raunata biyun.

Ya kuma ce an matasan sun kashe musu shanu 15, amma ya ce yana da wahala a iya tantance ainihin wanda ya kashe manoma 10, tun da babu wanda aka kama.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da kisan manoman guda 10.

Ya kuma ce, “Ofishinmu da ke Takum ya aiko wa hedkwatar rundunarmu rahoton cewa wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kashe manoma 10 a ƙauyen Jenuwa Gida.”