✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma da makiyaya: Shugaban Karamar Hukuma ya gana da masu ruwa da tsaki

Shugaban Karamar Hukumar Jama’ da ke Jihar Kaduna, Peter Danjuma Aberik ya ce rikice-rikicen da suke wakana a karamar hukumarsa sun janyo an zaftare kudaden…

Shugaban Karamar Hukumar Jama’ da ke Jihar Kaduna, Peter Danjuma Aberik ya ce rikice-rikicen da suke wakana a karamar hukumarsa sun janyo an zaftare kudaden da gwamnatin jiha ke ba su a matsayin ladabtarwa.

Shugaban, wanda ya bayyana haka yayin gana wa da masu ruwa da tsaki da suka kunshi shugabannin manoma da makiyaya da dagatai da shugabannin matasa da kuma jami’an tsaro da aka gudanar a dakin taro na karamar hukumar ya bayyana takaicinsa kan yadda matsalar tsaron ta haifar masa da koma baya wajen gudanar da manyan ayyukan ci gaba da ya kawo masu amfani musamman ga mutanen karkara.

Ya ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya dauko tsohon daftarin dokoki ne na jihar da aka rubuta tun shekarar 1958 inda dokar ta ce a rika zaftare kudin kasafin kananan hukumomin da ake rikici inda a yanzu hukuncin ya shafi kananan hukumomi takwas daga cikin kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar.

Kananan hukumomin  kamar yadda shugaban ya bayyana, sun hada da Chikun da Birnin Gwari da Sanga da Zangon Kataf da Sabon Gari da Jama’a wanda dukkaninsu a kan raba kasafinsu gida biyu ne a ba su rabi a matsayin horarwa inda ya ce ko kafin a cire kudaden, karamar hukumarsa ce mai daukar mafi karancin kasafi a duk kananan hukumomin jihar 23.

“Kashi daya kawai ake ba karamar hukuma yayin da daya kason gwamnati ke amfani da shi wajen magance matsalar rashin tsaro. Sai amfani da dan abin da na za a rasa ba wajen gudanar da ayyukansu.”

Shugaban ya kuma gargadi manoma da su kiyayi toshe labin shanu a yayin yin noma yayin da su kuma makiyaya aka ja kunnensu da su guji barin dabbobinsu suna yin ta’adi a gonakin manoma sannan a karshe ya yi kira ga iyayen yara da shugabannin gargajiya da su guji boye masu laifi a cikinsu a maimakon haka su rika mika su ga hukuma.

Daga karshe an bai wa mahalarta damar kawo mafita bisa mahangarsu inda aka yi muhawara kan matsayin kiwon kananan yara da batun daukar doka a hannu ko harin daukar fansa da sanya wa dabbobi guba ko toshe labin shanu da sauransu

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da manoma da makiyaya daga gundumomi goma sha biyu da ke karamar hukumar da jami’an tsaron sojoji da ’yan sanda da na DSS da jami’an Cibil Defence.