Najeriya ta umarci sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali da su gaggauta sakin jami’an gwamnatin da suka hambarar da ke tsare a hannunsu ba tare da wani sharadi ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma bukaci cikin wata 12 a kafa gwamnatin riko ta farar hula mai wakilici daga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki a Mali.
A cikin jerin sharuddan da ya gindaya wa masu juyin mulkin a yammacin Juma’a, Buhari ya ce sai sojojin sun cika sharuddan kafin su samu hadin kai da goyon bayan kasashen Yammacin Afirka da sauran sassa a hukumomin duniya da zai kai ga janye takunkumin da aka sanya wa Mali.
Buhari ya ce Najeriya da Kungiyar Rainon Tattalin Arzikin Afirka (ECOWAS) za su bayar da dukkannin gudunmuwar da ake bukata wajen gudanar da zabe da zai dawo da mulkin demokradiyya a Mali.
Shugaban ya yaba wa mai shiga tsakani na ECOWAS a rikicin, magabacinsa Goodluck Jonathan da sauran kasahen kungiyar kan jajircewarsu wajen kawo karshen rikicin da gaskiya.