✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin makiyaya da manoma ya yi ajalin mutum 38 a Nasarawa

Tun farko wani manomi ne ya kalubalanci wani makiyayi da ya saki dabbobinsa suka yi masa barna a gona.

Akalla mutane 38 aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da kananan yara da mata yayin wani harin ‘yan bindiga a garin Takalafiya da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.

’Yan bindigar wadanda har zuwa yanzu ba a kai ga gano su ba, na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke kan daidaikun mutane tun bayan wata takaddama da aka samu tsakanin Makiyaya da Manoma.

Rahotanni sun ce tun farko wani manomi ne a yankin Gwanja da ke makwabtaka da Takalafiya ya kalubalanci wani makiyayi da ya saki dabbobinsa suka yi masa barna a gona.

Yayin takaddamar ne kuma makiyayin ya rasa ransa dalilin da ya sanya rikici tsakanin bangarorin biyu.

Shaidun gani da ido sun bayyana wa manema labarai cewa tun daga wancan lokaci ne ake ganin harin sari ka noke da ke haddasa asarar dimbin rayuka wanda ake alakantawa da makiyaya.

Ko a ranar Alhamis din da ta gabata an ga yadda makamancin harin ya kashe mutane 4 yayin da a Juma’ar da ta gabata da Asabar din karshen mako ’yan bindigar suka sake gangami tare da kashe mutanen da yawansu ya kai 38.

Wata majiya ta bayyana cewa a asabar din da ta gabata al’ummar yankin suka gudanar da jana’izar mutane 38 da ‘yan bindigar suka kashe a kauyuka biyu.