Akalla mutum 13 sun rasu wasu da dama kuma suka jikkata a rikici tsakanin kabilun Lunguda da Waja da ke kan iyakar jihohin Adamawa da Gombe.
Rikicin ya auku ne kwanaki kalilan bayan harin Boko Haram, inda mayakan kungiyar suka kashe mutum 10 a kauyen Kwampre na Karamar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Sun kuma kona gidaje da makarantu da wuraren ibada, tare da raba mutum 5,000 da muhallansu.
- Dan majalisa ya halarci zaman Majalisa tsirara
- Yadda ’yan daban daji 30 suka fada tarko a Katsina
- Ganduje da Dantata sun sasanta Dangote da BUA
- Budurwar da ta fasa aure saboda Kwankwaso ta samu miji
Babban Sakatare Hukumar Agaji ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Muhammed Sulaiman ya ce rikicin na ranar Laraba ya yi sanadiyyar “kona kauyuka, kashe mutum 13 wasu da dama muka aka raunata su, cikin ’yan Waja da Lunguda.
“Kauyukan da abin ya shafa su ne Walu, Falu da Lamza, kuma yanzu hukumar ta yi wa ’yan gudun hijira 1,200 rajista domin tsugunar da su.”
Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar rikicin, tare da cewa an tura ’yan sandan kwantar da tarzoma domin samar da tasro da ganin komai ya daidaita.
Muhammed Sulaiman ya ce wadanda suka samu raunuka an kai su asibiti a Guyuk da Yola kuma an kafa sansanin wucin gadi na masu gudun hijira a wata makarantar firamare da ke Guyuk.
Ya roki gwamnati da hukumomin agaji da su taimaka wa mutanen da kayan tallafi domin saukaka musu radadin halin da suka tsinci kansu.
A shekara 2020, rikici tsakanin al’ummomin manoman ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da kone-kone a kauyuka.
Kabilun Lunguda da Waja da ke kan iyakar Jihohin Adamawa da Gombe sun dade suna zaune lafiya, kafin rikice-rikicen da aka fara samu tsakaninsu.