✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Kazakhstan ya ci rayuka fiye da 220 —Gwamnati

Shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya ayyana dokar ta-baci.

Gwamnatin Kazakhstan ta ce mutane 225 suka mutu a rikicin da ya barke a kasar, wanda ya fara daga zanga-zangar lumana a farkon watan Janairu, kan tsadar rayuwa.

Sabbin alkaluman sun bayyana cewar 19 daga cikin wadanda suka mutu a rikicin jami’an tsaro ne, sai kuma fararen hula da ’yan bindigar da suka yi wa zanga-zangar shigar bazata.

Bayan rikidewar zanga-zangar da aka fara zuwa tarzoma da kuma arangama tsakanin wani gungun mutane masu makamai da jami’an tsaro ne, shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya ayyana dokar ta-baci tare da neman agaji daga wata kungiyar gamayyar sojojin kasa da kasa da ke karkashin jagorancin Rasha.

Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito cewa, da fari dai mutane kusan 50 kawai gwamnatin Kazakstan ta ba da sanarwar sun mutu a rikicin da ya barke, wadanda ta ce 18 jami’an tsaro ne sai kuma ‘yan bindiga 26.

Sai dai a halin da ake ciki, sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta tabbatar, sun nuna cewar baya ga mutane 225 da suka halaka, wasu fiye da dubu 2 da 600 ne suka jikkata, 67 daga cikinsu kuma na cikin mawuyacin hali.

%d bloggers like this: