An sanya dokar hana fita na awa 24 a bayan barkewar rikicin kabilanci a garuruwan Nyuwar da Jessu da Yolde na Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar ne bayan kabilun Waja da Lunguda a garuruwan sun ba wa hamata iska, tare da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa tun da saniyn safiyar Talata.
- Ramadan: Tsohon Gwamna ya raba abincin biliyan N1.4 a Zamfara
- Ba son biyan albashi aka zabe ni ba —El-Rufai
- An yi awon gaba da fasinjoji 15 a Katsina
- Kar a manta da talakawa a lokacin Azumi — Buhari
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya sanar da kafa dokar a cikin wata takarda, wadda Babban Daraktan Labarai na Gwamnan Jihar, Isma’ila Uba Misilli, ya rattaba wa hannu.
Farfesa Njodi yace sanya dokar hana fitar ta zama dole domin a tabbatar da kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa tuni aka tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin tabbatar da doka da oda.
Zuwa lokacin kammala wanann rahoto, babu cikakken bayanin gani da adadin wadanda abin ya ritsa da su ko yawan asarar da aka yi a rikicin.