Fassarar Dalhatu Liman
Lokacin da na ji labarin rikicin ya sake barkewa a tsakanin kabilar Jukun da Tibi a makon jiya, a Karamar Hukumar Wukari a Jihar Taraba, na fadi a zuciyata cewa, “Wannan dadadiyar matsala ce.’’ A 1990, makonni kadan bayan na fara aikin jarida da Mujallar Citizens a Kaduna (yanzu ta ruguje), ni da abokin aiki, Tawey Zakka an dora mana nemo rahoto kan rikicin Jukun da Tibi wanda ya kazanta a waccan shekara a tsohuwar Jihar Gongola.
A cikin kwana biyu, mun gudanar da tattaunawa da dama a garuruwan Makurdi da Gboko da kuma Katsina Ala, kafin daga bisani mu dangana da garin Wukari. Mun sauka ne a otel din Taraba Hotel, inda muka share kwana biyar, kuma daga nan ne muke zagayawa zuwa lungu da sako da kuma wuraren da rikicin ya shafa a fadin karamar hukumar. Mun samu damar ganawa da wadanda rikicin ya shafa kai-tsaye da jami’ai da ma shugabannin al’umma, sai dai duk kokarin da muka yi na ganawa da Aku Uka na Wukari ya ci tura.
A lokaacin da muka shiga garin Wukari, galibin ’yan kabilar Tibi sun tsere zuwa Jihar Benue mai makwabtaka da jihar. Wata hanyar daji ce kawai a iyakar. Ana iya ganin ’yan kabilar Jukun zaune a cikin kauyukansu, sai dai mummunar barnar da rikicin ya haddasa a fili take, sakamakon yadda ake iya ganin yadda tarkacen konannun ababen hawa da gidajen da suka kone kurmus har ma da gonakin da aka lalata, suka mamaye garin na Wukari. A tashar motar garin Katsina Ala, an gwada mana yadda tsagerun duka bangarorin biyu, suka yi ta tare hanyar zuwa Wukari, suna binciken ababen hawa, kana su ware fasinjoji, lura da kabilarsu, sa’annan su kashe. Abokin aikina, Tawey, wanda dan kabilar Kuteb ne daga Takum, ya shiga cikin zullumi matuka, yana tunanin mai yiwuwa ne ya fada hannun tsagerun kabilar Tibi. Sai dai ni a nawa bangaren, ganin ina dan saurayi ko gezau ban yi ba, saboda ina ganin cewa ni ba dan kabilar Jukun ko Tibi ba ne, don haka ji nake ba abin da ya sha min kai.
Daga dukkan bayanai masu cin karo da juna, na kokarta na dora yatsuna a kan ainihin abin ke kawo wannan mugun rikici. Ya samo asali ne daga mafi munin matsalar nan ta batun dan kasa da bako da ke faruwa a Najeriya, wadda take da tsohon tarihi tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Dubban mutane masu hazaka na kabilar Tibi suna noma gonakinsu a yankin Wukari kuma suna bayar da ladan noman doya ga sarakunan gargajiya na kabilar Jukun.
Lokacin da Jukunawan suka farga da lamarin sai suka fara daukar ’yan kabilar Tibi a matsayin baki wadanda ba su cancanci su yi da’awar wasu damarmaki ko ’yanci a Wukari ba, musamman ma na siyasa. Abin da ya jawo haka shi ne a yayin tattaunawarmu shugabannin yankin da dama suna gani kabilar Tibi tana da kananan hukumomi da dama a Jihar Benuwai, amma su Jukun suna da daya ce kacal wato Wukari. Don haka bai kamata ’yan kabilar Tibi su shiga harkokin siyasar Wukari ba. Matsalar ita ce ’yan kabilar Tibi sun riga sun fi Jukun yawa a Wukari. A Gboko wani tsohon ma’aikaci ya nuna mana wata kidayar da wani jami’in mulki na Turawan Birtaniya ya gudanar a 1913, wadda ta nuna cewa kabilar Tibi tana da kashi biyu bisa uku na mazauna Wukari.
A takaicen takaitawa rikicin da ya barke a 1990, ya samo asali ne bayan gudanar da zaben kananan hukumomi da gwamnatin mulkin soja na Janar Babangida ta yi. Kamar yadda aka shaida mana, al’ummar Tibi ta ki shiga takarar shugabancin karamar hukuma, sai dai sun daddale a kan za su fitar da mataimakin shugaban karamar hukumar. To amma, Jukunawa sun tsaya kai-da-fata cewa hakan ba mai yiwuwa ba ne. Ana haka, kwatsam sai ga wani Bahaushe mai karfin hali, ya fito takarar shugabancin karamar hukumar. Sai ya yi sa’ar cin zaben tare da mara bayan ’yan kabilar Tibi. Kawai sai tsagerun Jukunawa suka kai masa hari, lamarin da ya sa ya shafe watanni yana jinya a asibitin Yola. Wannan ne silar yaduwar mummunan tashin hankalin kan titunan garin Wukari da kauyukan da ke kewaye.
Sai dai ko a lokacin ma, babu wasu alamun da suke nuna cewa al’ummomin yankin a shirye suke su zauna lafiya. A garin Katsina Ala, mun samu damar tattaunawa da Farfesa Mbendaga Jibo, a wani dan karamin otel dinsa, wanda bisa dukkan alamu yana tattare da shaukin ganin zaman lumana ya samu a wannan yanki. Ya ce kamata ya yi ’yan kabilar Tibi su rungumi dabi’ar nan ta kowanne dan Tibi ya auri mace ’yar kabilar Jukun, wanda kafin zuwan wasu zuriya a nan gaba, za a wayi gari babu dan dabilar Jukun ko daya da ya rage.