✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Jos: An kwaso daliban Gombe daga Filato

Matakin ya biyo bayan barkewar rikici a Jos a kwanakin baya.

Gwamnatin Jihar Gombe ta kwaso dalibai ’yan asalin Jiharta da ke karatu a Jami’ar Jos a Jihar Filato zuwa gida.

Matakin ya biyo bayan barkewar rikicin da ya faru a garin Jos a kwanakin baya, wanda har ya kai aka sanya dokar hana fita a garin.

Dawo da daliban ya biyo bayan umarnin da Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya ya ba Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar, Mista Meshack Audu laucu, kan tabbatar da debo su da kuma dawo da su gida.

Daliban sun dawo ne bisa rakiyar jami’an tsaron da gwamnati ta tura cikin motocin sufuri na Bas-bas guda hudu, domin su sami natsuwar cewa ceto rayuwarsu aka yi.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan isowar daliban, Kwamishina Audu Lauco ya ce ba a bayyana adadin daliban da aka kwaso ba sai nan gaba.

Daga nan sai ya yaba wa daliban bisa halin dattaku da kyawawan dabi’un da suka nuna wajen bin doka da oda a lokacin rikicin.

Wasu daga cikin daliban da suka zanta da Aminiya sun bayyana jin dadinsu ga Gwamnatin Jihar kan daukar matakin, inda suka ce ta tuna ta damu da rayuwar al’ummarta.