Rikicin jam’iyyar APC ya dauki sabon salo kan dakatar da tsohon Maitaimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Kudu maso-Kudu), Prince Hilliard Eta.
Jam’iyyar ta karyata sanarwar dakatarwar, da cewa wanda ya fitar da ita sojan gona ne kuma babu laifin da Eta ya yi balle ta dakakatar da shi.
“Muna nesanta kanmu da sanarwar, sannan wanda ya sa hannu a kanta ba shi ba ne, kuma bai taba zama sakataren jam’iyya ba, saboda haka sojan gona ne”, inji sanawarwar da Sakatarenta jam’iyyar, Bassey Ita ya fitar.
Eta shi ne shugaban rikon jam’iyyar na bangaren da Kwamitin Gudnarwar na Kasa (NWC) da aka rusa ya nada. Bangaren Eta na hamayya da shugabancin Victor Giadom wanda ya nada kansa a daya bangaren, ya kuma kira taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na kasa (NEC), inda aka rusa NWC a makon jiya.
- Rikicin APC: Shin Buni zai kawo karshensa
- Buhari ya karbi gurguwar shawara kan taron NEC —APC
- Buhari ya amince da shugabancin Giadom a APC
- Rikicin shugabanci: ’Yan sanda sun rufe hedikwatar APC
A makon jiya ne sakataren jam’iyyar daga bangaren Giadom, Francis Ekpenyong ya fitar da wata sanarwar amincewa da abin da ya ce dakatarwar da shugabannin mazaba da karamar hukuma na Jam’iyyar suka yi wa Eta bisa zargin cin dunduniyar jam’iyyar.
Sai dai kuma sanarwar da Bassey Ita ya fitar daga baya ta ce, “…wasikar ba daga Kwamitin Zartarwar Jam’iyyarmu a Jihar Kuros Riba ta fito ba kuma babu wani shiri na dakatar da jigon jam’iyyyar [Eta] da ake managa”.
Ya kara da cewa Eta cikakken dan jam’iyya ne, “kuma bai taba yin wani abu na karya kundin tsarin mulkin jam’iyya da zai sa a dakatar da shi ba”.