Gwamnatin Jihar Kwara ta umarci malaman makarantu 10 da aka rufe kan takaddamar hana dalibai sanya hijabi da su koma aji su ci gaba da koyarwa daga ranar Juma’a.
Gwamnain Jihar ta ce umarnin ya shafi shugabanni da daliban makarantun na mishan da ke samun tallafi daga kasashen waje.
- Mutum 56 na kwance asibiti bayan bullar wata bakuwar cuta a Kano
- ’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga suna shirin kai hari a Kaduna
- Zamfara: ’Yan bindiga sun yi wa mutane luguden wuta a kasuwa
Ta kuma ce duk malamin da ya ki bayyana a wurin aikinsa zai fuskanci fushin hukuma domin ba za ta lamunci rashin da’a ba.
Sanarwar dauke da sa hannun Amogbonjaye Peter, ta ce komawar ta zama tilas domin a shirya daliban ga manyan jarabawar dalibai da ke tafe.
Ya kuma gargadi masu ruwa da tsaki su guji daukar doka a hannunsu, yayin da ake ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da gwamnati.
Shugaban na TESCO ya ce Gwamnatin Jihar na ba da hakuri kan matsalar da dalibai suka samu sakamakon rufe makarantun, wanda ya ce an yi ne domin kauce wa fitina.
Ya kuma bukaci iyayen dalibai da sauran jama’a ad suka kwantar da hankalinsu, gwamnati na iya kokarinta don yi wa tufkar hanci a tattaunawarta da masu ruwa da tsaki.