✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin haraji ya lakume rai a kasuwar Katako

Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da raunata wasu biyar.

Rikici ya barke a kasuwar katako da ke garin Umuahia a Jihar Abiya.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewar rikicin ya barke ne a tsakanin ’yan kasuwar da jami’an Hukumar Tattara Harajin Jihar, kan biyan haraji N18,000.

  1. An kona rugar Fulani kan garkuwa da mutane
  2. KASU: Shin an rufe Jami’ar Kaduna saboda karin kudi?

Majiyar ta ce jami’an hukumar sun umarci ’yan kasuwar da su rufe shagunansu kan rashin biyan kudin, yayin da ’yan kasuwar suka koka kan yawan kudin da aka tsuga musu.

’Yan banga sun yi kokarin tilasta su su rufe shagunan, a garin haka ne, hargitsi ya kaure.

Majiyar ta ci gaba da cewa ’yan bangar sun harbe mutum daya tare da raunata wasu biyar.

’Yan kasuwar suka harzuka, nan take suka kone ofishi da motar ’yan bangar da ke cikin kasuwar.

Aminiya ta gano an garzaya da wadanda suka ji raunin zuwa asibiti.

Gwamnatin Jihar Abiya ta umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Janet Agbede da ya gudanar da bincike tare da gano musababbin rikicin.

Jawabin da Sakataren Gwamnatin Jihar, Chris Ezem, ya fitar ya umarci ’yan bangar su fice daga cikinta na wani lokaci, shugabannin kasuwar kuma su hada kai da ’yan sanda don gano bata-garin da suka tada rikicin.

Sanarwar ta ce dole ne bata-gari su daina kone kayan gwamnati, saboda aikata hakan babban laifi ne kuma da ke iya janyo tsattsauran hukunci ga masu aikatawa.

Ta kara da cewa za a hukunta duk wani dan bangar da aka samu da laifin cin zarafin mutane a jihar.