Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Hotoro Masallacin Juma’a a Kano ta bayar da umarnin a kamo mata jarumin fina-finan Hausa Sadiq Sani Sadiq.
Wani mai shirya fina-finai Aliyu Muhammad Hannas ne ya shigar da karar a gaban kotun kan cewa ya bai wa jarumin kudi domin ya yi masa aikin fim, amma ya ki zuwa don yin aikin, wanda a cewarsa, hakan ya ja masa asara mai yawa.
- Dalibin ajin karshe a BUK ya rasu a cikin makaranta
- An gano gawar mutum 30 da aka yi garkuwa da su a wani asibiti
Alkalin kotun, Mai Shari’a Sagiru Adamu, ya ce Sadiq ya bijire wa umarnin kotu duk da sammacin da aka ba shi, tare da like masa sammacin a kofar gidansa amma ya ki halartar zaman kotun.
Zuwa yanzu dai kotun ta bai wa dan sandan kotun umarnin kamo jarumin a duk inda yake tare da gurfanar da shi a gabanta.
Sai dai Sadiq Sani Sadiq ya bayyana cewa ba shi ya ke yin fim din ba, furodusan ne da kansa ya ce ya fasa yin fim din saboda wani dalili.
“Babu shakka akwai lokacin da furodusa Abdulaziz Dan Small ya zo tare da wani yaro ban ma san shi ba suka nemi na yi musu fim.
“Muka yi jinga akan abin da za su biya ni to a lokacin suka ba ni Naira dubu 100 a matsayin somin tabin kudin aikina. To sai da ranar da za mu fita aikin ta zo sai suka kira ni suka gaya min cewa ba za a iya daukar fim din ba saboda suna da wata matsala.
Shi ma a nasa jawabin, Furodusa Aliyu, ya bayyana cewa ya kai karar jarumin ne saboda ya yi iyawarsa a kan jarumin ya biya shi kudinsa amma abin ya faskara.
“Na ba shi kudi Naira dubu 100 don ya yi min fim amma wani dalili ya janyo ba a yi fim din ba don haka na nemi ya dawo min da kudina amma abu ya gagara.
“Daga baya sai ya bayar da Naira dubu 20. ba ni, hakan ya sa na kawo shi kotun don ta bi min hakkina,” inji shi.