Mutum hudu ne aka kashe a jihar Edo sakamakon rikicin fili tsakanin wasu unguwanni biyu da suka hada da Itsukwi da Imiakabu a Karamar Hukumar Etsako ta Gabas da ke jihar.
Rahotan na bayyana cewa, duk mazauna unguwannin sun ayyana cewa, suke da mallakin filin da ake rikicin. Wasu matasa na unguwar Imiakabu ne suka fara rufe hanyar zuwa unguwar Okpella da ke Ibie ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar rufe hanyar motocin fasinja, hakan ya yi sanadiyyar rikicin filin.
A yanzu haka an tura jami’an ‘yan sanda yankin kuma an kai wadanda suka jikkata asibiti don yi masu jinya.