✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Filato ya lakume rayuka 17 da gine-gine 85 —’Yan sanda

Rundunar 'yan sandan ta ce duk wanda aka kama na da hannu zai dandana kudarsa.

Kwamishinan ’yan sanda na  Jihar Filato, Mista Edward Egbuka ya ce mutane 17 ne suka mutu yayin da aka kone gine-gine 85 a rikicin da ya barke a Kananan Hukumomin Bassa da Riyom na jihar.

Egbuka, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya yi wa manema labarai karin haske kan lamarin bayan kammala taron gaggawa kan matsalar tsaro a jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Jos.

  1. Abin da nake fata daga shugabannin APC na kasa — Yari
  2. Ambaliyar Ruwa: Yadda Wasu Al’ummu Ke Kokarin Kare Kansu

A  cewarsa,  an kai hare-hare a kauyen Jebbu Miango na Karamar Hukumar Bassa inda aka kashe mutane biyar a ranar 31 ga watan Yuli sannan aka kashe wasu 12 ranar 1 ga watan Agusta a Tambora na Karamar Hukumar Riyom.

“An kai hare-hare musamman a kauyen Jebbu Miango a daren Asabar, 31 ga watan Yuli inda aka kashe mutane biyar tare da kone gine-gine akalla 85.

“Washegari da safe, an sake kai hare-hare a kauyen Tambora na Karamar Hukumar Riyom inda aka kashe mutane 12 tare da rusa wasu gidaje,” in ji shi.

Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa wasu jami’an tsaro kuma sun mutu a dalilin rikicin.

“Mai girma gwamna ya ba mu tsawon mako biyu da mu gabatar masa da rahoto kan rikicin tare da cafke wadanda ke da hannu a ciki,” in ji shi.

Ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama na da hannu zai dandana kudarsa.