✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin dan sarkin Hausawa da mahauta ya ci mutum biyu a legas

  Al’ummar Hausawan Unguwar Okokomaiko da ke daura da kasuwar Alaba-Rago a Legas sun wayi gari da tashin hankali, a sakamakon kisan wani mahauci da…

 

Al’ummar Hausawan Unguwar Okokomaiko da ke daura da kasuwar Alaba-Rago a Legas sun wayi gari da tashin hankali, a sakamakon kisan wani mahauci da ake zargin ɗan sarkin Hausawan yankin da hannu a ciki, lamarin da ya haifar da tarzomar da ta sake laƙume ran ƙarin mutum guda tare da ƙone fadar sarkin na Hausawan, Alhaji Adamu Ahmed Gaya.

Wani mazaunin unguwar mai suna Malam Husaini wanda ya shaida faruwar lamarin, ya shaida wa Aminiya cewa rikicin ya samo asali ne bayan da abokan ɗan sarkin mai suna Bashir Ahmad suka sayi tsire a wajan mahaucin suka kuma hana masa kuɗinsa, daga baya shi Bashir ɗin ya zo don ya karɓi wani tsiren sai mahaucin ya ƙi ba shi; ganin cewa abokansa da suka karɓa da farko ba su biya ba kuɗin sa. Nan take ɗan sarkin Hausawan da abokan nasa suka zubar da tsiran mahaucin a ƙasa.

“Ganin haka ne ya sanya mahaucin tare da wasu jama’ar gari suka kai ƙara wajen mahaifinsa, wanda ya ba su haƙuri, ya nemi ya biya kuɗin tsiren amma mahaucin ya ce ya yafe. Bayan da ɗan sarkin ya koma gida ne mahaifinsa ya yi masa faɗa, sai ransa ya ɓaci, inda ya koma wajan mahaucin tare abokansa suka yi masa barazanar sai sun hallaka shi. Taƙaddamar ta samo asali ne a daren Alhamis, inda a daren Juma’a sai aka sami wasu sun je suka harbe mahaucin da bindiga, inda ake zargi ɗan sarkin Hausawan da abokansa,” inji shi.

Bayan da abokan sana’ar mahaucin suka ga abin da aka yi wa ɗan uwansu, sai suka fusata suka halaka abokin ɗan sarkin a kasuwar Alaba-Rago kafin daga bisani suka je fadar sarkin Hausawa suka kunna mata wuta.

’Yan sanda sun yi nasarar kashe wutar rikicin a ƙarƙashin jagorancin kwamandan shiyyar ‘E’ ACP Auwal Musa. Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Legas, Imohimi Edgar ya ziyarci unguwar ta Okokomaiko, inda ya yi taron zaman lafiya da dattawan yankin tare da shuwagabannin mahautan; ya kuma ba su tabbacin cewa wanda ake zargi yana hannun  ’yan sanda don haka maganar ɗaukar doka a hannu tare da tayar da hargitsi ba ta taso ba.