Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya mika kananan yara kimanin 4,204 ga gwamnatocin jihohin Adamawa, Borno da Yobe.
A cewar asusun, galibin yaran wadanda rikicin ta’addancin Boko Haram ya shafa ne, kuma an sake mayar da su ga iyalansu da kuma ’yan uwansu domin su ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum.
- Edo: Gwamna ya fitar da ofishin mataimakinsa daga gidan gwamnati
- ’Yan bindiga sun harbe mutum 5 a wani masallaci a Kaduna
Babban Manajan kare hakkin yara na UNICEF da ke ofishinsu na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, Samuel Sesay, ne ya bayyana hakan a wani taron kwanaki biyu kan shirin aiwatar da yarjejeniyar mika mulki da aka gudanar a Maiduguri.
A cewarsa, an kulla yarjejeniyar ne a shekarar 2022 tsakanin Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dinkin Duniya domin ganin an cire yaran da ke da alaka da rikicin makamai daga wuraren da sojoji ke tsare da su.
Sesay ya ce, “Wannan Tsarin mataki-mataki ne kan yadda yaran da ko dai suka tsere daga hannun kungiyar masu dauke da makamai ko kuma shugabannin masu tayar da kayar baya suka sake su ko kuma suka mika wuya bisa radin kansu wadanda ba su dade ba a cikin cibiyoyin soji ko kuma a tsare kafin su sake haduwa da iyalansu da danginsu ko kuma aka sako su tare da hannanta su ga gwamnatin jiha ta hannun ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a don sake hadewa da jama’a yadda ya kamata.”
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo wacce ta samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Mohamed Hamza ta yaba da jajircewar hukumar UNICEF da sauran abokan hadin gwiwa na samar da wannan yarjejeniya tare da neman ganin an aiwatar da ita yadda ya kamata.
Kwamishiniyar, ta kara da bayyana wasu kalubalen da suka shafi ma’aikatar kan shirin aiwatar da ka’idojin da suka hada da zamantakewar yaran da ke da alaka da rikice-rikicen makamai da kalubalen tattalin arziki ga matasa.
“Masu ruwa da tsaki da ke nan dole ne su tabbatar da cewa an magance duk abubuwan da suka shafi kare hakkin yara gaba daya tare da cikakken mutunta ka’idodin jagoranci na ‘yancin yara, rashin nuna bambanci da kuma bukatar tabbatar da hakkinsu na rayuwa da ci gaba.” In ji kwamishiniyar.