Rikicin kabilanci da ya rikide zuwa na addini a baya-bayan nan a garin Billiri na Jihar Gombe ya yi sanadiyyar asarar dakiyoyi na sama da Naira milian 500.
Rahoton kwamitin bincike don gano musabbabin tashin-tashinar da gwamnatin jihar ta kafa ne ya sanar da haka bayan kammala aikinsa.
- Gwamnatin Buhari ta mai da barayi ’yan gata —IBB
- ’Yan ta’adda sun mamaye Kananan Hukumomi 10 a Katsina —Masari
A jawabinsa kan rahoton da kwamitin ya gabatar wa zaman Majalisar Zartarwar Jihar, Kwamishinan Yada Labaran Jihar Gombe, Julius Ishaya, ya ce wuraren ibada 33 ne aka kona wandada aka kiyasa a kan miliyan N33.1.
Kwamitin ya kuma gano mutum 41 da rikicin ya shafa da aka kashe wa Naira miliyan 94.6.
An kuma lalata shaguna 402 da wuraren kasuwanci 335 da shaguna mallakin karamar hukumar ta Billiri guda 66 wadanda kudinsu ya haura Naira biliyan 383.2.
Akwai kuma motoci da ababen hawa daban-daban da lambuna da aka salwantar, da kudinsu ya haura Naira miliyan 31.
Majalisar ta amince a abiya wadanda suka yi asarar diyya don rage musu radadin rayuwa.
Kwamishinan ya kara da cewa ita kanta Karamar Hukumar Billiri, an umurce ta da ta samar da wasu kudi dan a tallafawa.