Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ’yan jam’iyyarsa ta APC cewa za su iya tsintar kansu a irin halin da PDP ke ciki muddin ba su ajiye son zuciya sun magance rikicin da ke neman raba kanta ba.
Yanzu haka dai APC na fama da rikicin shugabanci a matakin kasa da ma wasu Jihohin, kasa da shekara daya kafin babban zaben 2023.
- Saudiyya ta zartar wa mutum 81 hukuncin kisa
- Mai shekara 98 din da ta shiga firamare na son zama likita a nan gaba
Sai dai a cewar Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa ranar Asabar ta bakin Kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya gargadi mambobin jam’iyyar da su kaucewa kiran suna da cin dunduniyar juna gabanin babban taron jam’iyyar na 26 ga watan Maris.
Ya kuma hore su da su ci gaba da jajircewa matukar suna so jam’iyyar ta ci gaba da jan zarenta a shugabancin Najeriya.
Buhari, wanda yanzu haka yake birnin Landan don ganawa da likitocinsa, ya kuma gargadi mambobin APC da su dauki darasi daga halin da ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP na ciki a yanzu na rashin hadin kai da rashin tsari.
Ya ce, “[PDP] Sun gaza a cikin shekara 16 a salon shugabancinsu da kuma salon adarwarsu. Tabbas muma muna da tamu barakar, kuma hakan ba sabon abu ba ne a kowace jam’iyya a fadin duniya.
“Amma duk jam’iyyar da ta sa son zuciya a gaba, za ta fuskanci mummunar makoma.
“Yayin da ake shirin zabukan 2023, muna bukatar tattauna muhimman batutuwa, kuma a kansu ya kamata mu mayar da hankulanmu, ba wai rikicin cikin gida ba.
“Dole mu kawo karshen kowane irin nau’i na tayar da zaune tsaye gabanin babban taron da zamu zabi sabbin shugabanni,” inji Shugaban.
Buhari ya kuma ce suna alfahari da cewa duk da karancin shekarunta, APC ta iya lashe zabuka har sau biyu a jere, yayin da kuma take ci gaba da kara fadada.