✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin APC: Shekarau ya sake doke Ganduje a kotu

Kotu ta yi watsi da karar da bangaren Ganduje ya shigar na neman rusa bangaren Shekarau da Barau Jibrin.

Bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibrin na Jam’iyyar APC a jihar ya sake kayar da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje a kotu.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ce ta sake yin watsi da bukatar da magoya bayan bangaren gwamnan suka shigar na menan ta soke hukuncin da ya tabbatar da halascin shugabancin jam’iyyar daga bangaren Shekarau.

A baya dai kotu ta tabbatar da zaben shugabannin Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano da bangaren Sanata Shekarau ya gudanar, hukuncin da bai yi wa bangaren gwamnan dadi ba, har suka daukaka kara.

A zaman sauraron shari’ar a ranar Alhamis, alkalin kotun, Mai Shari’a Hamza Muazu, ya sake yin watsi da bukatar bangaren Ganduje da kuma ta neman dakatar da aiwatar da umarnin kotun.

A ranar 3o ga watan Nuwamba ne dai kotun tabbatar da zaben shugabannin mazabu da kananan hukumomin jam’iyyar APC da bangaren Shekarau da Sanata Barau Jibrin ya gudanar, wanda mutum 17,908 suka kada kuri’a.

Kotun ta kuma yi watsi da bukatar bangaren Ganduje na neman soke zaben domin tabbatar da zaben da bangaren gamnan ya gudanar daga baya.