✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke kan hana ’yan mata rike waya a Kaduna

Dattawan gari sun amince a hana duk budurwar da ke rike waya ba tare da izinin iyayenta ba

Rikici ya barke kan dokar hana ’yan mata rike waya da sanya bakin gilashi a ido a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kura ta tashi a garin Kuriga da ke hanyar Kaduna-Birnin Gwari inda mazauna ke zargin ’yan Hisbah da wuce gona da iri bayan da farko sun hana ’yan mata sauraro kade-kade a waya.

“Tun da farko sai wasu jami’an suka suka haramta wa ’yan mata sauraron wake-wake a kan hanya wanda shi ma ya jawo hayaniya tsakanin ’yan Hisban nda matasa”, inji wani mazaunin garin.

Jihar Kaduna ba ta da ’yan Hisbah a hukumance, kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana, amma wasu al’ummomi na da su inda suke aikin tabbatar da kyawawan dabi’u.

Aminiya ta tuntubi Kwamandan Hisbah na garin Kuriga, Malam Ishaq Uwai Kuriga, wanda ya hsaida mata cewa yawan samun labarin fyade a garin ne ya sa Hisbah ta hana ’yan mata rike waya ba tare da amincewar mahaifansu ba.

“An gano cewa da waya ake yaudarar ’yan mata su rika badala shi ya sa dattawan kauyen nan suka zauna suka yanke shawarar hana duk wata yarinya rike waya ba da sanin iyayenta ba”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Mu ba ’yan sanda ba ne gwamnati ce za ta iya haramta wa mutane rike waya ba mu ba.

“Jama’ar gari sun fahimci cewa waya daya ce daga abubuwan da ake rudar ’yan mata da a yayin da karuwar matsalar fyade ke damunmu.

“Batun hana ’yan mata a kauyen sanya madubin ido kuma ba ni masaniyar a kai”, kamar yadda ya yi bayani.

Wani dattijo a garin, Abdullahi Kurig ya shaida wa Aminya cewa dattawan garin da wasu iyaye ne suka yanke shawarar hakan saboda yawan aikata fyade da sauran laifuka da ake yi wa ’yan mata.