✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke kan hana dalibai sanya hijabi

Rikici ya barke a yankin Machinga saboda hana dailibai mata Musulmi shiga aji sanye da hijabi a kasar Malawi. Mazauna sun shiga zullumi bayan wasu…

Rikici ya barke a yankin Machinga saboda hana dailibai mata Musulmi shiga aji sanye da hijabi a kasar Malawi.

Mazauna sun shiga zullumi bayan wasu da ba a sani ba sun banka wuta a ofihisn shugaban makarantar mallakin Kiristoci mabiya darikar Katolika, bayan ya ki barin dalibai Musulmi shiga aji a cikin hijabi.

Bayan ‘yan sanda a yankin sun tabbatar da barkewar rikicin a makarantar firamare ta Mpiri, wadda suka ce an kone ta kurmus.

Garin na da mazauna Musulmai da Kiristoci amma yawancin makarantunsa mallakin cocin Angilikan da Katolika ne.

Dokar kasar Malawi ta ba kayyade nau’in tufafin da dalibai za su sanya na makaranta ba, amma wasu makarantun kiristoci kan matsa cewa dalibansu ba za su sanya hijabi ba, kuma hakan da ya sha haifar da rikice-rikicen addini.

Zuwa yanzu da makarantun darikun Angilika da na Katolika da ke yankin sun yi barazanar rufewa sakamakon rikicin daya barke a makarantar ta Mmpiri.