Akalla daliget din APC biyu ne aka rawaito sun jikkata yayin zaben fid da gwanin ’yan Majalisar Dokokin Jiha a Karamar Hukumar Gbako ta Jihar Neja wanda ya rikide zuwa tashin hankali.
Aminiya ta gano mutum biyu daga cikin jami’an da aka kai wa hari da muggan makamai, na kwance a babban asibitin Lemu, hedkwatar Karamar Hukumar ta Gbako.
- NAJERIYA A YAU: Gudunmawar da kowa zai bayar wurin kawar da ta’addanci
- Muhammad Abacha ya zama dan takarar Gwamnan PDP a Kano
Majiyoyi da dama sun ce rikicin ya samo asali ne a lokacin da shida daga cikin ’yan takara bakwai suka zargi jami’ar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Lydia Kaura da yin magudi.
Kaura ta dage kan cewar dole ne a yi amfani da jerin sunayen daliget din da jam’iyyar APC ta bai wa hukumar.
Daya daga cikin ’ya’yan jam’iyyar, ya ce jami’ar INEC din ta dage kan sai dai a yi amfani da sunayen da ke hannunta wanda lamarin daga baya ya rikide zuwa rikici.
Wasu daga cikin ’yan takarar sun nuna rashin amincewarsu kan yadda ta kafe tare da rashin samun masalaha.
Wata majiya ta bayyana cewar, babu tabbacin ko jami’an hukumar da magoya bayan ‘yan takarar suka ladawa duka za su rayu.
Ya ce an dauke zaben daga hedkwatar Lemu a Karamar Hukumar Gbako zuwa Minna, babban birnin Jihar ta Neja domin ci gaba da zaben ranar Juma’a.
Har wa yau, bayanai sun bayyana yadda zaben fid da gwani na ’yan majalisar PDP shi ma ya rikide zuwa rikici a Karamar Hukumar Gbako.