Rikici ya barke a tsakanin mutanen gari da jami’an tsaro a Kano bayan ziyarar aiki da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar a ranar Litinin.
Rikicin ya barke ne jim kadan bayan shugaban kasar ya bude gadar sama a unguwar Hotoro a safiyar ranar.
- Sean Dyche ya zama sabon kocin Everton
- Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 34 a masallaci a Pakistan
Wani ganau ya bayyana wa Aminiya cewa, “Yanzu haka ’yan sanda suna ta harbi amma ba a harbi kowa ba; su ma mutane suna ta ihu suna jifan ma’aikatan.”
Ya kara da cewa bayan shugaban kasar ya bude gadar ya tafi ne wasu fusatattun matasa suka fara jefe-jefen duwatsu suna ihun “ba ma yi” tare da yunkurin zuwa bakin gadar domin rusa aikin, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
“Al’amarin ya biyo bayan hana su zuwa wajen da aka yi,” in ji shi.
Shugaban kasar ya kai ziyarar ce domin bude wasu muhimman ayyuka guda takwas da gwamnatinsa da ta Jihar Kano suka yi wa al’ummar jihar.
An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da kewaye yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya isa jihar domin kaddamar da ayyukan raya kasar.
A halin yanzu yana gidan gwamnatin jihar domin liyafar cin abincin rana da gwamnatin ta shirya masa.
Aminiya ta gano cewa tun da yammacin ranar Lahadi aka girke jami’an tsaro da na hukumar kiyaye hadura da ta zirga-zirgar ababen hawa ta jihar (KAROTA) a wasu hanyoyi don tabbatar da tsaro yayin ziyarar shugaba Buhari.
Hanyoyin da aka girke jami’an tsaron sun hadar da titin Sabo Bakin Zuwo, titin gidan Sarkin Kano, titin Ahmadu Bello da kuma titin Audu Bako.
Buhari ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawat 10 na Gwamnatin Tarayya da tashar sauke kayan jiragen ruwa a kan tudu da ke Dala.
Ya kuma kaddamar da cibiyar bayanai ta Jihar Kano da ke sakatariyar Audu Bako.
Sauran su ne Cibiyar Kula da Ciwon Daji da ke Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari a Giginyu da kuma Rukunin Gidajen Gwamnatin Tarayya a Gandun Sarki.