Akalla mutum biyar ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu yayin wani rikici mai kama da na kabilanci tsakanin ’yan acaba da ’yan kasuwa a yankin Dei-dei da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa wani hatsari da ya faru da dan acaban ne musabbabin daukar doka a hannu.
- Kotu ta umarci a kyale Nnamdi Kanu ya kalli wasannin Liverpool
- Batanci: ’Yan sanda sun gana da malaman addini a Gombe
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Akwai mutum biyar da na sani sun rasa ransu a wannan rikicin. Mun yi ta kiran jami’an tsaro su kawo dauki amma a banza.
“Mun damu matuka da wannan rikicin musamman yadda yake neman daukar salon na kabilanci,” inji shi.
Aminiya dai ba ta iya tantance gaskiyar yawan mutanen da aka kashe ba, amma daya daga cikin mutanen da lamarin ya shafa ya ce an kone masa gida.
’Yan kasuwar dai sun kashe dan acabar wanda suka zarga da yin tukin gangancin da ya yi sanadin mutuwar fasinjar da ya dauka.
Rahotanni sun ce sauran ’yan acaba sun yi yunkurin kai wa dan uwan nasu dauki, amma lamarin ya kazance daga bisani.
Wata majiyar kuma ta ce an kai wa direban tirelar da ta take matar hari, inda shi ma wasu suka taso don kare shi.
Sai dai daga bisani jami’an tsaro sun karasa wajen don kaucewa kara kazancewar rikicin.
Yayin rikicin dai an kuma kone gidaje da shaguna da dama.