✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikici na kara tsanani tsakanin ISWAP da Boko Haram

Boko Haram ta kashe wa ISWAP mutum 68 a rikicin ya faro bayan kan ha'intar ISWAP kan shirinta na yin mubayi’a ga shugabancin IS/ISWAP

Mayakan Boko Haram sun kashe matan ’yan ISWAP 33 a yankin Sambisa domin daukar fansar kashe Kwamandansu Aboubakar (Munzir) da wasu mayakansu 15 a fadan da suka fafata a tsakaninsu.

A ranar 3 ga Disamba ne Shugaban Boko Haram a tsaunin Mandara, Ali Ngulde, ya jagoranci mayakansu dauke da makamai suka kai hari ga mayakan ISWAP a Sambisa.

Rikicin ya faro ne bayan Boko Haram ta ha’inci ISWAP kan shirinta na yin mubayi’a ga shugabancin IS/ISWAP.

Zagazola Makama, kwararre kan yaki a yankin Tafkin Chadi, ya ce kungiyar ISWAP ba ta san Ngulde da tawagarsa sun yi musu kwanton-bauna ba, inda suka kashe akalla mayakansu 12, da dama suka tsere da raunuka, sannan Boko Haram ta kwace motocin Hilux hudu da makamai.

Daga nan ne Boko Haram ta kara tattara mayaka daga sansanin Abu Ikilima da ke Gaizuwa da Gabchari da Mantari da Mallum Masari domin kai farmaki a sashen ISWAP a Ukuba da Arra da Sabil Huda da Farisu, inda suka kashe wasu mayakan 23.

Bayan haka ne wani babban Shugaban ISWAP, Bana Chingori, ya jagoranci mayakan da suka kai harin ramuwar gayya kan ’yan Boko Haram a Farisu, inda ’yan ISWAP suka samu kama ’yan Boko Haram 15 ciki har da kwamandansu Aboubakar (Munzir) tare da kwace babura 7 daga hannunsu.

Daga baya kungiyar ISWAP ta ja da baya inda ta yi sansanin Izzah.

Daga nan ne suka koma garin Abbah mai tazarar kilomita 2 inda suka dunkule domin jiran Boko Haram.

Sai dai mayakan Boko Haram sun nufi inda matan ISWAP suke suka kashe 33 daga cikinsu.

’Yan gudun hijirar Borno 16,000 sun samu tallafi

A wani labarin kuma Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA), ta raba kayan abinci da na amfanin yau da kullum ga ’yan gudun hijira 16,000 a Jihar Borno.

Da yake jawabi a lokacin rabon kayan da Cibiyar Agaji ta Sarki Salman na Saudiyya ta bayar a sansanin ’yan gudun hijira na El-Miskin da ke Jere, Darakta Janar na Hukumar NEMA, Ahmed Mustapha Habib ya ce manufar hakan ita ce rage wahalhalun da ’yan gudun hijira suke fuskanta musamman lura da barnar da ambaliya ta yi a jihar.

Ya ce, kowane magidanci daga cikin su 16,000 ya samu kilo 25 na shinkafa da kilo 25 na wake da kilo 25 na gari da masara da taliya da sauransu.

Ya ce, NEMA za ta ci gaba da ba Gwamnatin Jihar Borno goyon baya wajen sake tsugunar da ’yan gudun hijirar a garuruwansu, yayin da sojoji ke ci gaba da samun galaba a yakin.

“A hankali al’amura na komawa daidiai saboda jajircewar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum. Sannu a hankali zaman lafiya da tsaro na komowa ga al’ummomi. Muna ganin aikin alheri daga KSRelief, cibiyar ta sake ba da gudummawar kayan abinci ga mutum 16,000 a Jihar Borno a karo na biyu,” in ji shi.

Da yake jawabi Gwamna Babagana Umara Zulum ya yaba wa Hukumar NEMA tare da nuna jin dadinsa da taimakon na Sarki Salman da Gidauniyar dangote suka kawo wa jihar.