Wasu abubuwan ban tausayi da mamaki sun auku a makon karshe na bara da makon farko na bana.
Wadannan abubuwa sun faru ne a jihohin Legas da Anambra, inda a Jihar Legas Kotun Majastare ta Yaba ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wani magidanci mai shekara 49 mai suna Lawrence Itakpe a kurkuku saboda zargin yi wa matarsa mai suna Rebecca kisan gilla.
- Buhari zai karbo ‘kyautar zaman lafiya’ a Mauritaniya
- Noman masara zai yi wahala a damina mai zuwa — Kamilu Sigau
Ana zargin Lawrence Itakpe da daba wa matarsa wuka a sassan jikinta agidansu da ke Unguwar Ajah ne inda ya yi sanadin mutuwarta.
Gardama a kan mallakar jakar ruwan leda a tsakanin ma’auratan da suka shafe shekara 11 a matsayin miji da mata har da ’ya’ya biyu a tsakaninsu ta sa mijin yanke wa kansa wannan danyen hukunci a daki bayan ya kulle ya hana kowa shiga.
Bayan sauraron karar, Alkalin Kotun Mai shari’a O. Y. Adefope ya amince da bukatar mai gabatar da kara Sufeton ’Yan sanda Haruna zargin a kurkuku zuwa ranar 31 ga Janairun nan domin ci gaba da sauraron karar.
A Jihar Anambra, kuwa jayayya a tsakanin Mista Ndubuisi Wilson Uwadiegwu da matarsa Ogochukwu Amene Uwadiegwu a kan sayan burodin da ’ya’yansu za su yi karin kumallo ne ya fusata mijin ya kama matar da duka har ya yi sanadin mutuwarta.
Wata majiya ta ce asirin Mista Wilson ya tonu ne a lokacin da ya yi kokarin binne gawar matar a cikin gidansu ba tare da sanin danginta ba.
Majiyar ta ce jayayya ta kaure ne lokacin da Uwargida Ogochukwu Amene mai ’ya’ya 5 maza 4 da mace 1 ta nemi mijinta Mista Wilson ya sayo wa ’ya’yansu burodin da za su ci inda ya ce babu kudi a hannunsa.
Sai matar ta yi amfani da kudin da ke hannunta wajen sayo burodin da ake bukata amma sai Mista Wilson ya zagaya cikin dakin dafa abinci a boye ya sace burodin ya cinye shi kadai ba tare da ya rage wa ’ya’yan ba.
Majiyar ta ce a yayin da matar ta nemi sanin dalilin aikata hakan sai ya rufe ta da duka tare da yin amfani da daba mata fasasshen gilashi a jikin hakan ya yi sanadin mutuwarta.
Sai dai a lokacin da Sashen Pidgin na BBC, ya zanta da Mista Ndubuisi Wilson, ya ce, “Kafin matar tawa ta mutu sun hada kai da daya daga cikin ’ya’yana maza da suke yawan cin zarafina da ya sa na ji haushin abin da suke yi min.
Gaskiya ne ta bukaci kudin sayan burodi kuma na ba ta sai dai ta sake bukatar wasu kudin na ki amincewa hakan ya haifar da jayayya a tsakaninmu na kama yaron da duka.
Cikin kuskure kuma na yanki matar da fasasshen gilashi ta samu rauni aka kai ta asibiti inda ta rasu,” in ji shi.
A Jihar Kwara kuma an kama wani matashi ne mai suna Issa Naigheti kan zargin hada baki da wasu mutum biyu wajen yin garkuwa da mahaifinsa mai suna Bature Naigboho inda suka karbi Naira miliyan biyu da rabi a matsayin kudin fansa.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi ya ce an kama Issa Naigheti a yankin Kambi a Ilori bayan garkuwa da mahaifinsa a garin Igboho/ Igbeti da ke Jihar Oyo.
Kakakin ’yan sandan ya ce matashi Issa bai musanta zargin da aka yi masa na garkuwa da mahaifinsa ba.
Ya ce yanzu haka ’yan sanda suna kokarin gano sauran mutum biyu da ake zargi da wannan danyen aiki.