Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin halsataccen Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.
Kotun ta kuma tabbatar da bangaren tsohon Gwaman Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da shugabannin da bangaren ya zaba a matsayin halastaccen shugabancin jam’iyyar APC a jihar.
- Ayyana dokar ta-baci kan matsalar tsaro babu amfani —Dingyadi
- An kama bindigogi 35 da masu muggan laifi 245 a Kano
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan daukaka kara da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kan hukuncin kotun da ta fara tabbatar da Alhaji Ahmadu Haruna Zago daga bangaren Shekarau a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na jihar.
Idan ba a matna ba a ranar 30 ga watan Nuwamba kotu ta amince da bukatar bangaren Shekarau na ayyana cewa bangaren Ganduje bai gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a matakin gudunduma ba.
A kan haka ne bangaren Gwamna Ganduje ya garzaya zuwa kotun daukaka kara yana neman a soke wancan hukuncin.
Amma da yake sanar da hukuncin a ranar Juma’a alkalin kotun, Mai Shari’a Hamza Muazu, ya yi watsi da bukatar bangaren gwamnan, ya kuma ci su tarar Naira miliyan daya na bata wa kotu lokaci.
Mai Shari’a Hamza ya tabbatar cewa bangaren Sanata Ibrahim Shekarau na jam’iyyar APC a Jihar Kano ya gudanar da taron zaben shugabannin jam’iyyar a matakin gundumomi da kananan hukumomin.
Ya kara da cewa bangaren Shekarau shi ne halastaccen shugabancin APC a jihar kuma yana da hurumin zaben shugabanni a matakin jiha.