Malam Musa Ado da ake wa lakabi da Kana Wuce Lahira, fitaccen mai sana’ar haka rijiya ce a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana gwagwarmayar da ya sha a sana’ar da irin abubuwan ban mamakin da ya gani yayin hakar rijiya:
Yaushe ka fara wannan sana’a?
To yanzu na kai shekara 40 ina sana’ar haka rijiya. Ainihin gidanmu ’yan noman lambu ne a garinmu na Ashura a Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi. A wancan gari na Ashura aka haife ni, shekara 70 da suka gabata.
Na fara wannan sana’a ce a Jagindi da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, inda wani mutum mai suna Malam Ladan Ba-Damuwa ya dauke ni, ya koya mini wannan sana’a. Daga nan da wani mutum mai suna Musa Tsiga ya ga kwazona, sai ya dauke ni ya kai ni wajen wani Bature muna haka rijiya yana biyanmu.
Shi ma wannan Bature ganin kwazona sai ya dauke ni ya kai ni wajen wani mutum mai suna Alhaji Isah Cikaji Zariya, wanda dan kwangila ne a lokacin. Daga nan na tashi daga Jagindi na koma Zariya wajen wannan mutum. Idan ya samu aikin kwangilar haka rijiyoyi, sai ya debe mu ya kai mu wajen aikin.
Sai mahaifina ya aika mini cewa in dawo gida. Daga nan sai Alhaji Isah Cikaji ya dawo da ni Saminaka aka dauko ni da kayan aikina aka damka wa Shugaban Sashin Ayyuka na Karamar Hukumar Saminaka a lokacin. Na ci gaba da aikin haka musu rijiyoyi tare da haka wa sauran jama’a a gidajensu.
Daga lokacin da ka fara sana’ar zuwa yanzu a takaice ka haka rijiyoyi kamar guda nawa?
A shekara ina haka rijiya akalla 30. Kuma daga lokacin da na fara wannan sana’a zuwa yanzu, akalla na haka rijiyoyi sama da 1000.
Ko taba haduwa da wasu abubuwan ban-mamaki?
Kwarai na ga abubuwan ban-mamaki da dama a wannan sana’a. Na farko a shekarun da suka gabata akwai wani mutum a garin Saminaka da ake kira Alhaji Tanimu Galma. Yana da wata rijiya lokacin sai aka kira ni domin in yashe ta, wannan rijiyar ce ta rufto mini dai har sai da na kwana biyu a cikin rijiyar kafin in fito, a kwana na uku.
Kuma yadda aka yi na fito shi ne matar mai rijiyar ce ta zo zubar da shara a cikin rijiyar, sai ta zuba sharar sai na ce waye ya zuba mini shara? Sai ta fita a guje ta je wajen mai rijiyar Alhaji Tanimu Galma ta ce masa ta ji an yi magana a cikin rijiyar. Da Alhaji Tanimu ya zo, sai ya ce waye a cikin rijiyar nan? sai na ce ni ne Musa. Sai ya ce Musa Kana-Wuce-Lahira. Daga nan aka kira yaran da suke taya ni aiki, suka zo suka fitar da ni.
Yaya aka yi ka kwana uku a cikin rijiyar?
Wato kasar rijiyar ce ta rufto mini a cikin rijiyar ta rufe ni. Kuma ina cikin aikin ne ban sani ba. Yaran da muke aiki da su da suka ga haka ta faru, suka yi ta kirana ni ina jinsu amma ni idan na yi magana, ba sa ji na. Ina cikin wannan hali sai na ci gaba da tura kasar baya, idan na gaji sai in tsaya. Haka na ci gaba da tura wannan kasa baya, har na samu na gusar da kasar da ta rufe ni na fito. Shi ne matar mai gidan ta zo zuba shara, sai ta zuba mini. Lokacin da abin ya faru yarona ya ce a bari idan na kwana uku ban fito ba, to shi ke nan na mutu. Domin shi yana ganin ina nan da rai.
Bayan haka akwai wata rijiya, ita ma wannan rijiya ina aiki sai na ga yarana ba za su iya kwashe ruwan ba. Sai na ce bari in fita in karbi wannan aiki na kwashe ruwan. Sai suka ce a bari a kawo inji. Da aka kawo inji na kunna na fita daga cikin rijiyar, injin ya janye ruwa. Sai na sake shiga rijiyar shi ne sai hayakin injin nan ya taba ni, sai da aka fito da ni daga cikin rijiyar. Sai da na kwana ban san halin da nake ciki ba.
Haka kuma akwai wani lokaci a Maraba, Abuja na ciro wadansu yara biyu da suka mutu a wata rijiya. A lokacin jami’an kashe gobara sun zo wajen tunda safe suna janye ruwan rijiyar, domin su fito da wadannan yara har zuwa bayan La’asar ba su samu fitar da su ba. A lokacin ina zaune sai aka bai wa babban jami’in ’yan sandan wajen labarina cewa zan iya ciro yaran. Nan take babban jami’in ’yan sandan ya zo da mota tare da yaransa suka dauke ni muka tafi. Ina zuwa da na leka rijiyar sai na hango yaran. Na ce a bar kwashe ruwan, na shiga na yi nitso a cikin ruwan rijiyar, na tsamo yaran na sa igiya na dauro su, na fito da su.
Har ila yau akwai wata yarinya da ta fada cikin wata rijiya a garin Saminaka aka rasa yadda za a a yi a fitar da ita, na zo na fitar da yarinyar. Bayan da na fito da yarinya, sai da na kwana uku, ban yi barci ba. Saboda idan na kwanta, sai in rika ganin gari yana juya mini. Sai da na je wajen wani mutum ya ba ni wani magani na sha.
Kadan daga cikin abubuwan mamakin da na gani ke nan cikin wannan sana’a.
Wadanne nasarori kake ganin ka samu a sana’ar?
Babu shakka na samu nasarori da dama a wannan sana’a, domin a takaice na koyar da yara wannan sana’a sama da mutum 30.
Kuma na samu rufin asirin a wannan sana’a domin na haifi ’ya’ya 16, amma 8 sun rasu yanzu 8 ne suke raye. Da wannan sana’a nake ci da rike iyalina.
Yaya za ka kwatanta sana’ar a da da yanzu?
Yanzu zamani ya canja mutane ba su cika son su haka rijiya a gidajensu ba. Sun fi son su haka rijiyar burtsatse. Amma wadansu masu dabara ko da sun haka rijiyar burtsatse suna haka rijiya a gidansu, saboda rijiyar burtsatse tana lalacewa, amma rijiya kuwa idan aka haka ta, aka gyara ta babu abin da yake samunta. Don haka masu dabara har yanzu, suna haka rijiya a gidajensu.
Wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati da masu wannan sana’a?
Ina kira ga gwamnati da sauran hukumomin samar da ruwan sha na gida da waje su tallafa mini, musamman kan irin gudunmawar da na bayar wajen samar da ruwan sha ga al’umma, ta hanyar wannan sana’a. Kamar yadda na fada tunda farko a yanzu na kai shekara 40 ina wannan sana’a kuma daga lokacin da na fara sana’ar zuwa yanzu, akalla na haka rijiyoyin da aka samu ruwan sha sama da 1000.
A yanzu idona ba na gani sosai, karfina ya kare, ga tsufa ya fara kama ni. Yanzu ina da shekara 70 a duniya. Don haka ina rokon a tallafa mini.
Kuma ina kira ga matasa masu wannan sana’a su kula su rike gaskiya da amana, idan suka yi haka za su samu ci gaba.