✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rigingimu 800 aka sulhunta cikin shekara guda a Yobe —Kwamitin Sulhu

An kafa Kwamitin domin shiga tsakani ba tare da shiga kotu ba.

Kwamitin Sulhunta rigingimu a Jihar Yobe ya ce ya magance rikice-rikice masu alaka da addini, zamantakewa, siyasa da wasu bangarori  na rayuwa fiye da guda 800 cikin shekara guda.

Shugaban kwamitin Babagana Kyari ne ya bayyana hakan a Damaturu babban Birnin jihar, yayin da yake karbar bakuncin ma’aikatan kungiyar ‘International Alert’ a ziyarar da suka kai wa kwamitin ranar Litinin.

Kyari ya ce tun daga lokacin da aka kaddamar da Kwamitin a watan Afrilun 2021, sun warware rigingimu iri-iri fiye da 800 a fadin jihar.

Kwamitin wanda aka kaddamar domin sasanta rigingimu ba tare da shiga kotu ko sabanin da ke haifar da doguwar shari’a ba, yana samar da maslaha da bangarorin za su amince da shi.

Kyari ya kuma ce kwamitin na aiki kafada da kafada da kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na waje domin samar da zaman lafiya tsakanin al’ummar  jihar ta Yobe.

A kan haka ne yake yaba wa kungiyar ta International Alert bisa gudummawar da suka ba wa kwamitin wajen sulhunta al’ummar Yobe.