A yayin da jihar Gombe ta sake karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 sama da 100,000 samfurin Modana, gwamnati ta samar da cibyoyi 67 a fadin jihar don yin allurar rigakafin.
Shugaban Kwamitin yaki da COVID-19 a jihar kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Manasseh Daniel Jatau, ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da allurar rigakafin cutar karo na biyu a ofishinsa.
- Yawi Modu: An kama dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo
- An kai hari gonar Obasanjo an yi gakuwa da ma’aikata
Manasseh Jatau, ya ce “Cibiyoyi shida aka ware a kowace karamar hukuma don yin rigakafin”.
Yace a karon farko an yi wa dattawa masu shekara 50 zuwa sama amma yanzu za a fara ne daga kan matasa masu shekara 18 zuwa sama.
Mataimakin gwamnan, ya kirayi wadanda suka karbi rigakafin a karo na farko da su je wuraren da aka ware don karbar kashi na biyu.
A cewarsa, rigakafin na farko na Astra Zenica da wanda aka kawo yanzu na Modana duk abu daya ne, sunan kamfani ne kawai bambanci, saboda haka mutane su je su yi a duk inda ya fi musu kusa.
Ya kuma hori al’umma da a har kullum su rika sanya takunkumi tare da da yawaita wanke hannu don kare kai.
Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su ba wa jami’an lafiya hadin kai domin karbar allurar rigakafin cutar ba tare da wata matsala ba.