’Yan jam’iyyar APC bangaren Sanata Kabir Marafa a Zamfara sun ce matakin da kwamitin rikon ya dauka na korar shugabansu Alhaji Sirajo Garba karan-tsaye ne ga ikon kotu.
Kwamitin rikon jamiyyar da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ke jagoranta, a wasikar da Sakataren Jam’iyyar na kasa, Sanata John J. Akpanudoedehe, ya saka wa hannu y ace Garba ya ki yin biyayya ga umurnin jam’iyya.
A ranar 25 ga watan Yuni, 2020, Shugabannin APC suka zartar cewar kada wani dan jam’iyyar ya shigar da kara kotu, wadanda kuma suka shigar da karar su janye domin bai wa kwamitin rikon damar yin sulhu a cikin gida.
Sai dai kuma kakakin bangaren Marafa, Alhaji Bello Bakyasuwa ya fada wa ’yan jarida a ranar Laraba cewa, Kotu mai hurumin aiwatarwa ta rushe shugabannin jam’iyyar da ’yan bangaren kuma ta ce a gudanar da sabon zabe, don haka matsala kwamitin za ta haifarwa APC a Zamfara.
“Ba ku da masaniya kan hukuncin kotu na rushe bangarorin biyu da umurnin sake sabon zabe? Hakan ba zai zama karan-tsaye ga hukuncin kotu ba?
“Ko da yake har yanzu babu wanda ya tunkare mu da maganar. mun ga takardar ne kamar yadda kuka gan ta a kafar sada zumunta. Za mu fadi matsayarmu idan aka tunkare mu a aikace” inji shi.
Da aka tambaye shi sun janye karar da suka kai jam’iyyar, sai ya ce, “Wa ya ce mu janye? Kuma yaushe? Babu wani lokaci da hedikwatar jam’iyyar ko wani daga kwamitin rikon ya ce mana mu janye.
“Zai yiwu hedikwatar jam’iyyar ta ce abokan jam’iyyarmu su dakatar da mu? Zai yiwu APC karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta ki bin hukuncin kotu?
“Ina tunanin an yi kwamitin riko ne domin a magance matsalolin jam’iyyar ba kara su ba.
“Ba za ka magance matsala ba in har ka shiga cikin ko ka goyi bayan wani. Za ka iya magance matsala ne ta hanyar adalci da gaskiya”, kamar yadda ya ce.
“Goyon bayan wani bangare a wannan lokacin zai haifar da lalacewar jam’iyyar APC ne kawai a Zamfara, kuma bana tsammanin Kwamitin Mai Mala zai yarda haka ta faru”, inji shi.