✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#RevolutionNow: Jami’an tsaro sun kama mutum 60 a Abuja

Masu zanga-zanagar sun ce an kama fiye da mutum 60 daga cikinsu a Abuja

Jami’an tsaro, wadanda suka hada da ’yan sanda da sojoji, sun kama masu zanga-zangar lumana ta #RevolutionNow akalla 60 a Abuja, babban birnin tarayya.

Masu zanga-zangar lumanar na bin titunan manyan biranen jihohin kasar nan ne domin tuna zagayowar shekara guda da gudanar da zanga-zangar lumana ta farko ta #RevolutionNow, wadda aka yi  a ranar5 ga watan Agusta, 2019.

Wanda ya shirya gangamin, Omoyele Sowore, a shafinsa na Twitter ya ce jami’an tsaro sun ci zarafin masu zanga-zangar lumanar a Legas.

“’Yan sanda sun tsayar da masu zanga-zangar lumana ta #RevolutionNow a Gadar Third Mainland. Sun tauye musu hakkinsu na dan Adam ta hanyar tursasa musu zuwa ofishinsu”, inji shi.

Wani jagoran zanga-zangar Deji Adeyanju ne ya ce jami’an tsaro sun kama fiye da mutum 60 daga cikinsu a Abuja.

Ana gudanar da zanga-zangar ne dai a birane daban-daban na Najeriya.