Kungiyar Daliban Najeriya (NANS), ta nesanta kanta daga zanga-zangar RevolutionNow da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, yake jagoranta.
Kakakin NANS, Adeyemi Azeez, ya shaida wa ’yan jarida a ranar litinin, a Abeokuta, Jihar Ogun, cewa babu ruwan kungiyar da duk wani haramtaccen taro da sunan zanga-zanga.
“Sowore na amfani da kafar labaransa wajen yada karairayi da jita-jita a kan ’yan siyasa da ba ya so,” kamar yadda NANS ta zarge shi.
Kungiyar ta ce sakarci ne ga duk dan Najeriya da ke neman tunzura ’yan kasa su yi wa Gwamnatin Tarayya bore a daidai lokacin da take fama da matsalolin tsaro.
NANS ta kuma bukaci dalibai da matasan Najeriya da su zamto masu bin doka, kar su bari wani ya yi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye.
Kungiyar kuma ta yi tir da abubuwan da ta ce ’yan sandan rundunar FSARS ke yi a kasar nan.
Daliban sun zargi ’yan sandan FSARS da kwace da kuntata wa ’yan kasa ta hanyar talauci da kashe mutanen a lokacin da suka ga dama, ba tare da doka ta yi aikinta ba.