Kotun Shari’ar Musulunci da ke Tudun Wada a Zariya, Jihar Kaduna ta daure iyayen yaran da aka yi masu fyade saboda karar da wadda ake tuhuma ta kai su gabanta.
Tun da farko dai, an zargi matar, mai suna Amina Umar ne da bata yara hudu ’yan kasa da shekara bakwai ta hanyar sa musu yatsa a gabansu.
- Kasashe 7 da ake amfani da harshen Hausa bayan Najeriya
- ‘Na kashe dan acaba saboda na samu kudin sayen data’
To sai dai reshe ya juye da bushiya lokacin da wacce ake zargin tam aka iyayen yaran a kotu kan zargin bata mata suna.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdurrahaman Ibrahim ya ce mai karar ta shigar da karar bata mata suna da tsoratarwa da kuma cin zarafi, wadanda suka saba da sassa na 137 da 216 da 232 na kundin Penal Code.
Kotun dai ta ce ta same su da aikata laifukan har guda ukun da ake zarginsu da aikatawa sannan ta yanke masu hukuncin daurin watanni biyar a kan kowane laifi ko kuma zabin biyan tatar N7,000 ga kowacce tuhuma sai kuma tarar N50,000 na bata suna.
Iyayen yaran sune Shu’aibu Haruna mai shekaru 75 da mahaifiyarta Hussaina Sani.
Amina Umar na zaune ne a Gonar Ganye a unguwar Tudun Jukun da ke gundumar Tukur Tukur, a Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.
Yaran dai sun bayyanawa Aminiya haka ne a cibiyar bincike da kula da yaran da aka ci zarafinsu da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya.
Likitoci dai sun yi bincike tare da tabbatar da cewa biyu daga cikin yaran sun sami matsalar rashin iya rike fitsari a yanzu haka, kuma daya daga cikin yaran tana fitar da jini ta gabanta, sakamakon raunin da ta samu.
Mahaifin yaran mai suna Sha’iabu Yunusa Sha’aibu, ya shaida wa wakilinmu cewa suna bukatar gudumuwa daga cibiyar don daukar matakin bin kadin bata musu yara da aka yi.