Za a kece raini tsakanin kungiyar kwallon kafa Real Madrid da da Villareal, a ranar Alhamis a wasan da sakamakonsa ka iya zama abin biki ga ’yan wasa, shugabanni, mahukunta da dimbin masoya kungiyar Madrid a fadin duniya.
Real Madrid dai a yanzu ce ke saman teburi da maki 83 a wasa 36, sai mai biye mata, Barcelona mai maki 79 a wasa 36. Ke nan saura wasa biyu a kammala gasar.
Yadda wasan zai kaya
Ita kuma abokiyar karawar Real Madrid, wato Villareal ita ce ta biyar, inda take da maki 57 a wasa 36.
Za a fafata wasan ne da misalin karfe 8 na dare.
Idan Real Madrid ta doke Villareal, wato ta samu maki uku, to ta lashe gasar La Liga ke nan da maki 86, ko da kuwa ta rasa wasan karshe, kuma ko da Barcelona ta lashe sauran wasanninta.
Idan Madrid ta lashe wasan, ta hada maki 86 da wasa daya a hannu. Ita kuma mai biye mata, Barcelona idan ta lashe wasanta na yau, ta hada maki 82. Ke nan ko Madrid ta rasa wasanta na karshe wanda za ta fafata da karamar kulob, Leganes wanda ita ce ta ukun karshe, zai kasance tana da maki 86.
Ita kuma Barcelona idan ta lashe wasanta na yau, sannan ta lashe wasan karshe, za ta hada maki 85.
Idan Real Madrid ta yi kunnen doki anjima, ita ma Barcelona ta yi kunnen doki, Real Madrid ta lashe gasar dai.
Amma idan Real Madrid ta yi kunnen doki, Barcelona ta lashe wasanta, za a jira wasa na karshe a ga yadda za ta kaya.
Ke nan wasan yau na da matukar muhimmanci a wajen Real Madrid. Maki ukun take bukata kawai domin hankalinta ya kwanta.
Idan Madrid ta lashe gasar bana, za ta kara kafa tarihi a kan wanda take da shi na yawan lashe gasar, inda wannan zai kasance na 34.
Daga dawowa hutun COVID-19 zuwa yanzu Real Madrid ta lashe wasanninta tara da ta buga.
Tsakanin Real Madrid da Villareal a tarihi
A wasannin da suka buga a tsakaninsu, Real Madrid ta lashe wasa 22, Villareal ta lashe 4 an yi kunnen doki 12.
Ke nan za a iya cewa Real Madrid na da tarihi mai karfi a kan Villareal.
Sai dai wannan wasan ana iya cewa daban ne, domin kamar yadda Madrid ke bukatar maki uku domin lashe gasar Laliga, ita ma Villareal mai maki 57 na bukatar wasan domin samun gurbi shiga gasar UEFA ta badi.
Ko Villareal ta lashe sauran wasanninta guda biyu, zai zama tana da maki 63 ne. Ke nan ba za ta iya kamo na hudu a teburin ba, wato Sevillla wadda ko a yanzu take da maki 66. Ke nan Villareal ba ta za ta samu damar zuwa gasar Zakarun Turai ba.
Amma kungiyoyin da ke biye mata guda biyu Getafe na shida a tebur da Real Sociedad na bakwai a tebur duk suna maki 54 a yanzu. Ke nan maki uku ne a tsakaninta da su yanzu.
Sai kulon din Atletic Club da ke na takwas yanzu da ke da maki 51 ita ma.
Kasancewar ana bukatar kulob hudu a kasar Spain da za su shiga Gasar Zakarun Turai, sannan guda biyu su shiga Gasar Uefa.
Ke nan akwai kalubale mai girma a gaban kungiyar Villareal, inda dole ta dage damtse wajen tsira daga neman kwace mata gurbi da masu binta ke yi.
Kungiyar Real Mdrid
An kafa kungiyar a 6 ga Maris na 1902, inda real a yaren Spain ke nufin sarauta, Madrid kuma Babban Birni.
Ta fara wasa a filinta na Santiago Barnabeu tun a shekarar 1947.
Kulob din na da kimar Dala biliyan 4.2 kamar yadda aka kimanta ta a bara.
Ta lashe Laliga guda 33, Gasar Zakarun Turai guda 13 Copa del Rey guda19 da sauransu. Amma rabonta da lashe Laliga tun kakar 2016-2017.
A yanzu Zinedine Zidane ne kocinta, Sergio Ramos ne kuma kyaftin.
Kungiyar Villareal
An samo sunan ne daga Vila-real Club de Futbol, wanda ake takaitawa da Villareal. An kirkiri kulob din ne a shekarar 1923 a yankin Castellon, kuma tana wasa ne a filin Estadio de la Ceramica.
Ta taba zama ta biyu a Gasar Laliga ta kakar 2007-2008, sannan ta taba zuwa wasan kusa da karshe a Gasar Zakarun Turai a kakar 2005 zuwa 2006.