Eden Hazard zai bar Real Madrid a ranar 30 ga watan Yuni bayan da ya amince kungiyar ta soke sauran kunshin yarjejeniyarsa da ta rage.
Ya koma Real Madrid kan fan miliyan 89 a 2019, sai dai wasa 54 ya buga a lig, ciki har da shida da ya buga a kakar bana.
- NDLEA ta kama mutum 26 kan zargin safarar kwayoyi a Gombe
- Kano: Abba ya ba da umarnin kama masu ‘dibar ganima’ a wuraren da ya yi rusau
Hazard mai shekara 32 ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta karkare a Yunin 2024, amma yanzu ya amince zai bar kungiyar kafin wa’adin ya cika, sakamamkon yawan jinya.
A lokacin da yake tsaka da jinya, dan wasan tawagar Belgium ya lashe Champions League da Club World Cup da European Super Cup da La Liga biyu da Copa del Rey da Spanish Super Cup.
Cikin wasa 76 da ya yi wa Real Madrid a dukkan fafatawa, ya ci kwallo bakwai, wanda ake ganin kwazonsa ya yi kasa sosai.
Dan kwallon ya buga wasa 352 a Chelsea da cin kwallo 110, inda daga nan kungiyar Stamford Bridge ta sayar wa Real Madrid shi.