Bayan barin Real Madrid da Zinedine Zidane ya yi a matsayin kocinta, kungiyar ta sake daukar Carlo Ancelotti karo na biyu a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Ancelotti ya shiga jerin masu horarwa da suka jagoranci kungiyar sau biyu, bayan Zinedine Zidane.
- Barcelona ta dauki Aguero daga Manchester City
- Za mu kamo masu garkuwa da daliban Islamiyya — Gwamnatin Neja
Tuni Carlo Ancelotti ya warware kwantaraginsa da kungiyar Everton da ke buga gasar Firimiyar Ingila, don sake dawo wa Real Madrid.
Rahotanni sun bayyana sabon kocin ya rattaba hannun zama a kungiyar na tsawon shekaru uku, har zuwa karshen kakar wasanni ta 2024.
A tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 Ancelotti ya jagoranci Real Madrid inda ya lashe gasar cin Kofin Zakarun Turai a 2014.
Yanzu dai Carlo Ancelotti ya sha gaban masu horarwa irin su Mauricio Pochettino, Antonio Conte da Raul Gonzalez, wandanda ake sa ran wani daga cikinsu zai karbi ragamar kungiyar.