A daren jiya na Lahadi ne Real Madrid ta sake samun nasarar lashe kofin Super Cup a wasan karshe da ta fafata tsakaninta da abokiyar hamayyarta da ita ma take buga gasar La Liga a Sifaniya, Athletic Bilbao.
Real Madrid ta lallasa Bilbao da kwallaye biyu babu ko daya a wasan karshe na gasar da ya gudana a filin wasa na King Fahad da ke birnin Riyadh a Saudiyya.
- Musanta juna biyu: Ina hikimar A’isha Buhari?
- N100m muka biya kudin fansa a kauyenmu —Al’ummar Nahuche
Kwallon da Luka Modric ya jefa da kuma wacce Karim Benzema ya sakada a bugun daga kai sai mai tsaron raga su ne suka bai wa tawagar ta Carlo Ancelotti damar nasara tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci.
Kwallon Modric ita ce ta farko da dan wasan mai shekaru 36 ya zura a cikin wannan kaka, dai dai lokacin da ake tararrabi kan makomarsa a kungiyar da ta kafa lashe kofin Zakarun .
Nasarar lashe kofin na Spanish Super Cup ya nuna cewa zuwa yanzu Real Madrid na da irin kofin har guda 12 banbancin guda daya tal tsakaninta da Barcelona wadda ke da tarihin dage kofin sau 13.
Yayin wasan na jiya dai, ita ma Bilbao ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga amma kuma ta gaza yin nasara, yayin da golan na Real Madrid, Thibaut Courtois ya yi amfani da doguwar kafarsa wajen tare kwallon da Raul Garcia ya buga masa a tsakiya.
Tarihi ya nuna cewa Athletic Bilbao ta lashe kofin karo da suka hada da wanda ta ci a shekarar 1984, 2015 da kuma na 2021.
Ita dai gasar wannan kofi da ake kira Supercopa de España a yaran Sifaniya kuma ake kira Spanish Super Cup, ana buga ta ne tsakanin kungiyoyi hudu da suka hada da kungiyoyin da suka lashe gasar La Liga, Copa del Ray da kuma kungiyoyin da suka zo na biyu a gasannin biyu.