Real Madrid ta doke Celta Vigo 2-0 a wasan mako na 30 a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar a Santiago Bernabeu.
Saura minti uku su je hutun rabin lokaci, Marco Asensio ya ci kwallo, sannan Eder Militao ya kara na biyu a minti na uku da suka koma zagaye na biyu.
- Rasha ta kori jami’an diflosmasiyyar Jamus sama da 20
- Dalilin da ba za a iya kwaso ’yan Najeriya da suka makale a Sudan ba
Da wannan sakamakon Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki 65, ita kuwa Celta tana nan da maki 36 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ce kan gaba a matakin farko mai maki 73, wadda za ta karbi bakuncin Atletico Madrid ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Real Madrid da Celta sun fara wasa a bana a La Liga ranar 20 ga watan Agustan 2022, inda kungiyar Santiago Bernabeu ta je ta ci 4-1.
Real ta ci kwallayen ta hannun Karim Benzema a bugun fenariti da Luka Modric da Vinicius Junior da Federico Valverde.
Ita kuwa mai masaukin baki, Celta ta zare daya ta hannun Iago Aspas a minti na 23 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Sakamakon wasannin da aka buga ranar Asabar 22 ga watan Afirilu:
- Osasuna 3 – 2 Real Betis
- Almeria 1 – 2 Athletic Bilbao
- Real Sociedad da Rayo Vallecano
- Real Valladolid 2 – 1 Girona
- Real Madrid 2 – 0 Celta Vigo
Karawar mako na 30 ranar Lahadi 23 ga watan Afirilu
- Elche da Valencia
- Barcelona da Atletico Madrid
- Real Mallorca da Getafe
- Sevilla da Villarreal