✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta kora PSG gida; Man City ta tsallaka zagaye na gaba

Real Madrid ta kafa tarihi ta hannun dan wasan gabanta Benzema, wanda ya zura kwallaye uku rigis a ragar PSG.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kafa tarihi wajen doke PSG da ci 3-1 a Gasar Zakarun Turai.

Kungiyoyin sun sake barje gumi a karo na biyu a gasar ne a filin wasa na Santiago Bernabeu da ke kasar Spain.

Dan wasan gaban PSG Kylian Mbappe ne ya fara zura mata kwallo a minti na 36, wanda hakan ya ba ta damar samun kari a kan kwallon da suka zura a wasan farko.

Sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Real Madrid ta yi ta maza, inda dan wasanta Kareem Benzema ya jefa mata kwallaye uku ragas.

Wasan ya dauki hankalin ’yan kallo, ya kuma kayatar da magoya bayan Real Madrid.

Yanzu haka dai Madrid ta kora PSG gida da adadin zuwa mata kwallaye 3-2.

Manchester City ta je gaba

Manchester City kuwa ta karbi bakuncin Sporting  CP a filin wasa na Etihad, amma wasan an tashi babu ci.

An murza leda na tsawon minti 90 amma babu kungiyar da ta yi nasarar jefa wa abokiyar karawarta kwallo a raga.

Amma duk da haka Manchester City ta samu zuwa zagaye na gaba, sakamakon lallasa Sporting CP da ta yi da ci 5 a wasan farko da suka kara.