Real Madrid ta tabbatar da kammala daukar dan wasan baya, David Alaba daga Bayern Munich a kyauta.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Intanet.
Dan wasan mai shekaru 28 ya rattaba hannu a kan kwantaragin da ya kulla yarjejeniyar zaman kakar wasanni biyar a kungiyar da zarar kwantaraginsa da Bayern Munich ya kare a ranar 30 ga Yuni, 2021.
Tun bayan bude kasuwar cinikayyar ‘yan wasa a watan Janairu, Jaridar MARCA ta ruwaito cewa, Real Madrid ta shiga zawarcin David Alaba, wanda har ta kai ga ya amince tare da kulla yarjejeniyar baka tsakaninsa da kungiyar.
Yanzu dai Alaba ya zama cikakken dan wasan Madrid bayan gwajin tabbatar da koshin lafiyarsa da aka yi.
Rahotanni sun bayyana cewa, Manchester City, Paris Saint-Germain, Liverpool da Chelsea na daga cikin manyan kungiyoyin Turai da suka nuna sha’awar daukar dan wasan.
Ana sa ran Munich za ta maye gurbin Alaba da dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, Dayot Upamecano.
Bayan kammala daukarsa, Alaba zai buga wa Real Madrid wurare da dama da suka hada da gurbin baya, gurbin baya daga hagu da kuma tsakiyar fili.
David Alaba ya zura kwallaye 35 a tsawon zamansa a kungiyar Bayern Munich.