✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta fara yunkurin korar kocinta

Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fara tunanin korar kocinsa Julep Lepotegui nan da karshen wannan wata. Jaridar AS ta Sifen ta ruwaito…

Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fara tunanin korar kocinsa Julep Lepotegui nan da karshen wannan wata.

Jaridar AS ta Sifen ta ruwaito cewa tuni mahukunta kulob din suka fara tunanin kocin da zai maye gurbinsa da zarar sun kore shi.  Jaridar ta kara da cewa daga cikin kocin da kulob din ya fara zawarci sun hada da tsohon kocin Chelsea Antonio Conte.

Kocin Madrid Julep dai yana shan suka daga magoya bayan kulob din ganin yadda kawo yanzu kulob din ya koma matsayi na 4 a gasar rukunin La-Liga bayan ya buga wasanni 4 a jere ba tare da ya samu nasara ba.

Haka kuma magoya bayan kulob din ba su ji dadin yadda kulob din CSKA Mosko na Rasha ya doke na Madrid a gasar zakarun kulob na Turai a kakar wasa ta bana ba.  Hakan ya zubar wa  Madrid mutunci a idon masoya kwallon kafa. Sai dai rahotannin da ke fitowa daga kulob din sun nuna idan Kocin bai yi kokari nan da karshen wannan wata ba, ko shakka babu za a sallame shi.

A ranar 28 ga wannan wata da muke ciki ne kulob din zai yi wasa mafi zafi da FC Barcelona, wasan da ake wa lakabi da “El-Clasico”.

Masana harkar kwallo sun yi hasashe daga ranar ce kocin zai san matsayinsa, na ci gaba da zama ko kuma a sallame shi.